HANYAR KARIYA DAGA KAMUWA DAGA WANNAN CUTA TA FITAR DA RUWA
- A daina amfani da magunguna barkatai, ba tare da shawarar likita ba, musamman waÉ—anda ake kira da antibiotics da kuma steroid
- A ƙauracewa zinace-zinace
- A daina tura ko kuma zura wani abu a cikin gaba al’aura
- Wadda take da cutar, ta je ta nemi magani a asibiti saboda ka da ta shafawa wani ko wata.
KAMMALAWA
Zubar ruwa daga gaban mace yana damun mata kwarai da gaske, amma ba kowanne ba ne yake na cuta ba. Idan na cutar ne kuma, ana iya warkewa idan an sha magani. Kuma har yanzu, a likitance, ba a tabbatar da cewa ana É—aukar cutar a banÉ—aki ba.