Kalolin Abincin Dake Kara Lafiya Ga Mai Ciki Da Jaririnta:

Assalamu alaikum warahmatullah, barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon shirin namu da yake zuwar muku a wannan shafi namu mai albarka na howgist.com

Kula da cin abinci mai kyau da lfy da Gina jiki Yana da matukar anfani ga lafiyar mu ,a bangare daya kuma mace mai juna biyu ita yafi dacewa ta dimauce da cin abinci mai Gina jiki don Lafiyarta da kuma jaririn da take dauke dashi .

Don haka ga wadansu nau’ikan abinci masu Gina jiki daya dace da mai juna biyu ta dage da cinsu domin samun koshin Lafiyarta da jaririnta.

KWAI

Kwai na daya daga cikin abinci dake Samar da sinadarin Gina jiki ,masana sun tabbatar da cewa kwai na kunshe da kusan dukkanin sinadarin da ake bukata na Gina jiki da ingantaciyar lafiya ga mai juna biyu .

ABUBUWAN DA SUKA DANGANCI WAKE

Wanan ya hada da farin wake ,jan wake ,peas,waken soya ,koran wake ,gyada ,da dai sauransu ,wadanan dangigin wake na kunshe da sinadarai masu matukar anfani da mahinmanci wajan Gina jiki da suke hada dasu ,iron ,folate ,B9,da calcium ,wanda mai juna biyu ke bukata don samun ingantaciyar lafiya tare da jaririn da take dauke dashi .

GANYAYYAKI

Ganyayyaki kamar irinsu alayyahu,kabeji,salad,yakuwa,zogale,rama,yadiya,tafasa,da dai sauransu suna kunshe da sinadarai masu matukar anfani da mahinmanci wajan Gina jiki wanda suka hada da ,vitamin C,Bitamin K,Calcium,iron,folate da kuma potassium.babu shakka mai ciki tana da bukatar wadanan sinadarain da muka ambata a sama ,saboda yadda suke taimakawa masu juna biyu da bunkasa garkuwar jikin su

NAMA

Nama babu shakka ko ba’a fada ba ,kowa yasan nama Yana daya daga cikin abinci mai Gina jiki ,nama na dake da sinadarin , iron, choline,B_bitamin ,wanda ake so mata masu juna biyu su rinka ci dayawa ,rashin samun wanan sinadarin mussanman iron da muka ambata a farko Yana da hadari ga mai juna biyu ,don kuwa masana suna gargadi rashin sinadarin iron ga mai ciki na iya haifar mata yin bari ,ko kuma haifar yamushin jinjiri .

RUWA

Ana son mace mai juna biyu ta yawaita shan ruwa akai akai don Lafiyarta dana jaririnta ,idan mai juna biyu ta Fara samun karancin ruwa a jikinta ya kan iya haifar mata da ciwon kai ,kasala,faduwar gaba,ko razana wasu lokutan kai harma da baccin rai.
A bangare daya kuma samun isasshan ruwa na taimakawa MATA wajan cushewar ciki da kariya daga cutar dakan shafi mafitsara .
Wanan shine ku cigaba da kasancewa damu domin samun cigaban abubuwan daya kamata masu ciki su rinka ci.

Allah yaqaremu da lafiya yasa duk wata mai juna biyu ta haihu lafiya

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!