ME YAKE JANYO YAWAN ZUBAR DA RUWAN A HQ DIN MACE
Kamar yadda na faɗa a baya, shi yawan zubar da ruwan zai iya kasancewa na cuta ko kuma wanda ba na cuta ba.
Abubuwan da suke janyo zubar da ruwa na cuta sun haɗa da
- Juna biyu (ciki)Amma fa wani lokacin, juna biyu yana iya janyo zubar ruwa na cuta
- Yin amfani da ƙwayoyin tsarin iyali
- Lokacin jinin al’ada
- Abubuwan da suke janyo zubar ruwa na cuta sun haɗa da
- Shan magunguna barkatai, musamman waɗanda ake kira da Antibiotics ko Steroid da sauran su
- Cututtuka a jiki kamar Diabetes (ciwon suga), HIV, Cancer da sauransu
- Juna biyu (ciki): yana iya janyo zubar ruwa na rashin lafiya da kuma wanda ba na rashin lafiya ba
- Saduwa da wanda yake ɗauke da cutar: namiji zai iya dauka daga wurin mace, sannan mace ma za ta iya dauka daga wurin namiji
- Zinace-zinace
- Yawan wanke cikin gaba da wani sinadari vaginal douching
- Masan tangaran toilet seats
- musamman idan wadda take dauke da cutar ta yi amfani da shi kuma ba ta wanke masan ba. Amma fa har yanzu ba a tabbatar da wannan hanyar ba
- Idan mace tana da, ko kuma, tana aikata ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan, to za ta iya kamuwa da wannan cuta ta zubar da ruwa.