SHAWARA GA YAN MATA KAN SAMARIN SU:

Yawancin Ƴan Matan yanzu suna jin tsoron su rasa samarinsu shiyasa sai sanda saurayi yaga dama sannan zai turo iyayensa ayi maganar aure. Yakamata duk wanda yace yana sonki da gaske!. Idan har kin tabbatar kema kina sonsa zaki iya aurensa. ko da zaki rasa shi, koda zai rabu dake, Kice ya turo iyayensa gidanku a ajiye magana.

Turo iyaye ba shine Aure ba. Amma kada kiji tsoro kice masa ya turo a ajiye magana idan ya gudu daga baya. saboda dama yaudara ce ta kawoshi wajenki kada kidamu kansa ya cuta domin Iyayensa ya zubarwa da mutumci ya mayar dasu kana nan mutane.

Kada kiji tsoron rasa wani saurayin idan Maza dubu za su ce suna sonki da aure to kice musu bakya da ikon aurar da kanki don haka ya turo iyayensa a ajiye magana koda ba da wuri za’ayi auren ba kici gaba da addu’a watarana Allah zai kawo miki wanda zai tsaya ya aureki.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!