Yadda Ake Kira Da Private Number Da Kuma Abinda Ake Nufi Da Private Number:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, a yau zamuyi bayanine dangane da lambar boye, lambar boye wani tsarin saiti ne da ake saitawa a cikin waya bangaren saitin layi wanda ke baiwa mutum damar kiran wani lamba ba tare da anga asalin lambarsa ba, madadin haka sai dai a ga “hidden number” wato boyayyen lamba.

Lokuta da dama in dai mutum ya san waya ya kuma jima yana amfani da ita, ya san cikinta to ba ya da bukatar shiga cikin settings domin boye lambarsa.

Kawai wasu lambobi zai danna da farko kafin ya kira lambar da yakeson ya kira take zakaga kira da boyayyiyar lamba.

Yadda Ake Kira Da Private Number:

Kiran Private Number da USSD Code ta hanyar amfani da USSD code zaka iya kiran duk lambar da kakeso ta private ba tare da wanda ka kira ya ga lambarka ba.

Domin yin hakan saika danna #31# sannan ka rubuta lambar mutum ta biyo bayan #31# din saika danna wajen kira.

Ga dai yadda abin yake a aikace.

Zaka bude phone app din wayarka saika danna #31# sai lambar wanda kake son kira ya biyo baya
Misali #31#081458xxx sai ka kira
Kiran yana shiga wanda ka kira din kai tsaye zai ga kira ya shigo masa ta private number wato boyayyen lamba zanso ka kula, ka kuma sani cewa da yiwuwar asirin lambarka ya tonu kai har ma da sunanka muddin mutum yana amfani da manhajar truecaller ko ya latsa wadansu USSD Codes kafin ya daga wayar taka.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!