Gwamnatin Nigeria Zata Fara Bawa Dalibai Tallafin Bashi Marar Kudin Ruwa Ga yadda Tsarin Zai Kasance
A ranar Litinin shugaba Tinubu yasa hannu akan sabuwar Dokar da zata bayar da izini Gwamnatin tarayya ta fara bayar da Bashi wa ‘yan makaranta, wato Rance ko Aron Kudi wa ‘dalibai a Nigeria. Shugaba Tinubu yasa hannu wa Dokar ne wacce Speaker House of Representatives Barrister Abdul-Hakeem Olufemi Gbajabiamila ya dauki nauyi, kuma Dokar ta tsallake karatu na ‘daya da na biyu har na Uku a Majalisar Wakilai sati biyu da suka wuce.
Rancen kudin za’a dinga bayar dashi ne wa ‘yan Nigeria kadai.
Kuma Non interest Loan ne, wato babu Kudin ruwa a ciki, idan dubu 200,000 ka karba haka za’a biya a lokacin biya babu ‘kari ko na Naira ‘daya.
Za’a dinga bayar da Bashin ne wa ‘daliban gaba da Sakandare, kamar NCE, Diploma, Degree, Masters, PhD da researchers da sauran su..
Duk shekara ne za’a dinga baka damar ka karbi abinda kake ganin zai wadatar da kai na tsawon wannan shekarar, shekara ta gaba ma ka sake karba, har shekarar kashe da zaka gama makaranta, amma da ka’ida tare da ‘kaidi (Limit).
Shugaba Tinubu ya fada wa ‘dalibai a lokacin Kamfen dinsa cewa “idan na zama shugaban kasa zan samar da wata hanyar da zaku dinga samun Aron Kudi daga Asusun Gwamnatin kasar ku, maimakon ku koma gida sai lokacin da kuka samu kudi kuyi karatu, toh zamu nemo hanyar da zaku samu sauki rashin Kudi ba zai hana ku karatu ba”.
Idan ‘dalibi ya karbi Kudin yana da damar ya biya a lokacin da yake karatu, ko kuma ya bari sai bayan ya gama ya samu aiki ya dinga biya kadan kadan, za’a bayar da wasu shekaru a cikin su ‘dalibi ya biya kudin da ya karba bayan ya samu aiki daga baya.
Za’a ajiye kudaden ne a Hannun Ma’aikatar ilimi ta ‘kasa (Ministry Education).
Wannan dai Bill ne, Doka ce yanzu a Nigeria.
Yaya zaka bi ka karbi Bashin? me dame ake bukata, idan ka cika yaushe kudin zasu zo Account ‘dinka?
Tsarin karban Bashin ‘Yan Makaranta a Nigeria:
1- A ‘karkashin dokar da shugaba Tinubu yasa wa hannu, za a kafa Bankin Ilimi na Najeriya (Education Bank) wanda shi ne zai rika tsarawa da sa ido da kuma aiwatar da bayar da Bashin karatun.
2- ‘Dalibi zai iya samun bashin ne ta hannun ma’aikatar ilimi ta kasa, kuma ba zai fara biyan bashin ba sai ya samu aiki bayan kammala karatu da kuma hidimar kasa ta shekara daya (NYSC).
3- Dalibai za su iya neman bashin ta hanyar makarantun da suke, inda makarantun za su shige musu gaba.
4- Za a tantance dalibi domin aga ko ya cancanci karban bashin.
5- Dokar ba za ta amfani duk dalibin da zai yi karatu a wajen Najeriya ba, ko kuma mai karatu a makarantar da ba ta gwamnati ba.
Kafin ka cancanci samun rancen:
- Sai ka samu gurbin karatu (Admission) a wata babbar makaranta ta jiha ko ta tarayya – walau jami’a ko kwalejin kimiyya da fasaha( polytechnic ) ko kwalejin ilimi ko kuma makarantar koyon sana’r hannu.
- Dole ne kudin da kake samu ko kuma iyayen ka suke samu ya kasance kasa da naira dubu 500 a shekara.
- Dole ne dalibi ya gabatar da masu tsaya masa, akalla mutum biyu wadanda za su kasance ma’aikatan gwamnati da suka yi shekara 12 a aiki.
- ‘Dalibi zai iya gabatar da lauya wanda ya kai shekara 10 da aiki ko kuma wani ma’aikacin shari’a.
Idan dalibi ba makarantar gwamnati yake karatu ba toh ba zai samu wannan rance ba.
Babu maganar wariya ko nuna bambanci ga wani dalibi bisa jinsi na mace ko namiji ko addini ko wata nakasa.
Bashin zai kasance na biyan kudin makaranta ne kawai.
Waɗanda ba za basu Bashin ba:
- Idana kaci bashin Bankin Ilimin a baya kuma ka ki biya, ba za’a sake baka ba.
- Idan har wata makaranta ta taba kama ka da laifi, ko kuma wata kotu ta taba samun ka da laifin rashin gaskiya ko zamba, to ba ka cikin wadanda za su ci moriyar tsarin.
- Idan an taba kama ka da laifin da ya danganci miyagun kwayoyi, wannan ma zai hana ka samun rancen.
- Idan har wani daga cikin mahaifanka, walau uwa ko uba ba su biya bashin da aka ba su ba na dalibtar to ba za a ba ka ba.
Yadda za ka biya bashin
- Yana daga cikin aikin Bankin Ilimin ya rika bibiyar wanda aka baiwa bashin ya san lokacin da zai gama karatun, da aikin yi wa kasa hidima har zuwa samun aiki domin tabbatar da mutum ya fara biya a lokacin da ya dace.
- Bankin zai hada kai da inda kake aiki domin tabbatar da ana yankar kudin da ya kamata a rika sanya wa a Asusun da ya ba ka bashin.
- Duk wanda aka bai wa bashin zai fara biya shekara biyu bayan kammala aikin yi wa kasa hidima (NYSC).
- Za a rinka yankar kashi 10 cikin dari na Albashin ka ana biya.
- Idan aikin kanka da kanka kake yi, wato ba a karkashin wani kake aikin ba, to gwamnati za ta rinka karbar kashi 10 cikin dari na yawan ribar da kake samu a duk wata, inda za ka rika kai kudin da kanka bankin.
- Kwana sittin da zaman ka mai sana’ar kai za ka mika bayanan harkokin kasuwancin ka ko aikin naka, misali Bankin ka da wajen da kake zaune da abokan sana’ar ka da wadanda suke da hannun jari a ciki da sauran bayanai.
- Idan ka ki biyan bashin za a iya yi maka hukuncin daurin shekara biyu a gidan yari ko tarar naira dubu 500 ko kuma a hada maka duka biyu.