Yadda Zakayi Register Na CAC Da Kanka

Assalamu alaikum barkanmu da wannan lokaci da fatan kowa yana cikin koshin lafiya.

A yau zanyi bayani akan yadda zakuyi Register na CAC da kanku wato yadda zaku mallaki CAC Certificate

Me yasa zakayi Registration na cac 

Shi CAC yanada matukar amfani fiyeda yadda mutum yake tunani saboda idan bakayi wannan registration dinba kuma zaka rasa abubuwa da yawa wani lokacimma zai iya kaika gidan yari idan case ya hadaaka da hukuma. 

Ba kamar yadda mutane shuka daukabah cewa amfanin cac kawai shine don cika tallafi koneman bashin gwamnatin tarayya a a ba iya wannan bane amfaninsa amfaninsa yanada matikar yawa da saikayi zaka sani kadan daga ciki 

  • Zaka iya samun bashin gwamnatin tarayya koh na jaha mai waya 
  • Zaka iya samun bashin daga banki 
  • Zaka iya samun tallafi kyauta daga gwamnati koh kungiyoyi 
  • Zaka iya kare kanka dashi idan hukuma ta tambayeka shedar registan kasuwancinka 
  • Zai bawa customers naka daman yadda dakai idan kuma wani ne kakeson kufara kasuwanci zai iya shiga ya dubah yaga saboda KYC know your customer 

Idan kun lura zakuga wasu shagunan suna mannasa a bango idan sunyi saboda customers su gani

Dadai wasu abubuwa masu matukar amfani wanda inka shiga site din zaka ganewa idonka 

Da farko idan kanason yin registan CAC akwai wasu hanyoyi kamar haka 

  • Na farko zakaje office dinsu inkaso
  • Na biyu kaje cafe inkaso 
  • Na uku shine wanda zakayi da kanka inzaka iya 

Toh akan na ukun zamuyi magana insha Allah 

Yaya zakayi Registration na cac da kanka a wayanka 

Da farko zaka shiga https://www.cac.gov.ng/  home page zai budema saika shiga inda akasa online registration kamar yadda zaka gani a kasa

Kana shiga zai budema acan kasa zakaga inda aka rubuta register ta gefe saika taba zai budema wurin login amma kai tunda sabone bazaka taba nan bah saika dubah inda aka rubuta SIGN UP saika shiga 

Kana tabaya zai budema inda zakayi register ma ana zaka shigar da bayanan ka bawai bayanan kasuwanci bah naka da kake amfani dashi zakasa 

Sai kayi register ka tattabar da cewa kasa email mai amfani domin dole saikayi verify nashi 

Idan kasa saikaje kan email din ka zaka message din saikayi verify nashi idan verified shine zai baka daman shiga wannan website din  

Kana gama verified saikazo ga shiga wurin login domin kana login zai budema wurin kamar haka 

Toh daga nanne zaka fara registration na CAC ka wato na kasuwancinka 

Da farko saika taba kan NEW NAME RESERVATION anan zakasa sunan kasuwancinka 

Saika sunan da kakeso guda biyu idan bakasamu dayanbah saika samu dayan sannan saika biya naira daribiyar sannan kayi 

Idan ka cike duk bayanai saika generating na remita kabiya da katin bankinka basaikaje banki bah zaka iya biya da ATM dinka 

Bayan ka biya zaka ganshi a pending sai sai an approved koh rejected sannan ka ganshi a reserved koh denied 

Idan aka approved zaka cigaba da registration naka kenan domin ana nunama sunan ya samu don haka sai Registration da code din da suka turoma

Idan zaka fara registration zaka shiga inda aka rubuta reserved idan ka shiga sai start new registration with reservation code saika shiga kasa wannan code da aka baka domin cigabah da registration

Kana shiga zai bakah inda zaka cika bayanan ka na kasuwancinka saika fara cikawa 

Kana gama cika bayanan kasuwanci ka sai kazo kan upload na document naka wanda akeso ka sa akwai abubuwa guda hudu da akeso kayi scanning ka daura 

Akwai  I,D card national I’D card koh voters card ko driver license

Sanna kwai sahannunka zakayi signing a takarda saika yi scanning ka upload 

Sannan akwai passport naka wato photon ka zaka dauka ka tura 

Sannan sai wasu document idan akwai bukata amma ba dole bane wannan ukun sune dole 

Kana gamawa saika danna save and continue daga nan zai kaika inda zakaga duk bayanan daka cika saika dubah kaga ba kuskure idan kaga bah kuskure saikai submit nashi zaikaika inda zaka biya kudi 

Shimadai ta remita zaka biya kudi adadin da akasa a wurin idan ka biya saikai submit kajira approved

Wannan bayanin gaba daya munyine akan business name wanda akwai wasu da dama bayanshi naga dai kaman munfi yin shine amma akwai saura sunkai biyar innaga toh saika dubah wanne yakamata kayi saika dubah home page inda zaka fara registration akwai wani PDF guidelines ne gaba dayansu tundaga farko har karshe saika dakko shi kana dubawa kanayi harka gama.

Allah ya bada sa a 

©️ A.I.H 

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Check Also
Close
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!