Yadda Zakayi Apply Na Nigerian Navy Recruitment 2024
Assalamu alaimu barkanmu da wannan lokaci da fatan kowa yana cikin koshin lafiya.
Rundunar sojojin Ruwan nigeria wato Nigerian Navy, sun bude shafinsu domin sake daukan sabin ma’aikatan ta na shekarar 2024
Rundunar ta bude shafin ne tun a ranae 2/1/2024 sannan kuma zata rufe a rana 2/2/2024
Ga masu bukatar wannan aikin sai su duba abubuwan da ake bukata wajen cikawa.
Abubuwan da ake bukata wajen cikawa
- Dole ka kasance dan Nigeria
- Dole shekarunka su kasance daga 18 zuwa 30
- Dole ya kasance baka da aure ko da
- Dole ya kasance kana da Jarabawa a kalla 5Credit da english da maths
- Dole tsayin namiji karya gaza 1.69 meters mata kuma1.65 m
- Dole sai kana da BVN
- Dole sai kana da NIN number
- Dole ya kasance baka da wata larura ta musamman
- Dole ya kasance baka taba aikata wani lefi ba.
Yadda zaka nemi aikin
Domin neman aikin Danna Link dake kasa
https://portal.joinnigeriannavy.com/Identity/Account/Register
Idan ya bude zai baka wajen da zakayi Register sai kayi Register da email sannan kasa passoword, amma password din ya kasance ka hada suna da number da symbols, misali Arewa@1234
Bayan kayi Register daga nan sai kayi login sannan ka fara shigar da bayanan ka.
Allah ya bada sa’a