Yadda Zaka Nemi Aikin Nigerian Immigration Cikin Sauki

Assalamu alaikum jama’a barkanmu da wannan lokaci da fatan kowa yana cikin koshin lafiya.

Rundunar hukumar hige da fice ta nigeria wato Nigerian Immigration service NIS, ta bude shafinta domin sake daukan sabbin ma’aikata na sabuwar shekarar 20223.

A sabo da haka ne rundunar take sanar da duk mai sha’awar shiga aikin dayabi matakan data shardanta domin ya nemi wannan aikin.

Rundunar ta kasa wannan aikin ne zuwa bangarori guda uku wato categories A,B,C sannan kowane categories akwai jerin ayyukan da za’a iya nema gwargwadon Qualification dinka.

Ga yadda matakan suke:

Category (A): SUPERINTENDENT CADRE

  • I. SI conpass shine wanda suke da kwarewa akan fannin lafia wato doctors kuma sun gama NYSC ɗinsu wanda suka karanci MBBS kenan
  • II. DSI conpass: shikuma wannan wanda suka karinci sanin magun guna wato pharmacist kuma suka gama NYSC ɗinsu
  • III. ASI conpass o8 shikuma shine wanda duk wani mai degree koh HND wasu fanni daban kaman computer science, physics, history da sauransu zasu cika 

Category (B) INSPECTOR CADRE 

Sukuma wanna sune na masu NCE da kuma diploma koh Advance NABTEB 

  • I. Inspector Of Immigration (II) CONPASS 07
  • (Nursing): Mai son wannan mukami dole sai ya kasance yayi karatu a bangaren Registered Nursing (RN) ko bangaren Registered Midwifery (RM) ko duka bangarorin biyu RN da RM. Sannan kuma dole ya kasance yana da Certificate na Nursing and Midwifery Council of Nigeria (NMC).
  • II. Mataimakin Sufeto na Shige da Fice (Dukkan),
  • General Duty, CONPASS 06: Mai son wannan mukami dole sai ya kasance yayi Notional Diploma (ND) ko NCE.

Category (C) ASSISTANT CADRE

  • I. Immigration Assistant iii compass shikuma idan kanada GCE koh NECO da sauransu wato wanda suka gama secondary school kuma sukeda credit guda huɗu 4 kada ya wuce zama biyu 
  • II. Immigration Assistant iii conpass o3 shikuma wannan shine na masu trade certificate a driving koh mechanic kuma suma ya kasance sun gama secondary school wato SSCE 

Abubuwan da ake bukata wajen cikewa

  • Dole ya kasance kaiɗan Nigeria ne 
  • Kanada National I’D card 
  • Yakasance kanada takardan makarantanka a hannu na abunda kakeso ka nema 
  • Dole ya kasance kanada certificate daga asibiti na medical fitness kuma asibitin ya kasance na Gwamnati 
  • Dole ya kasance kanada ɗabiu mai kyau kuma ba a taba kamaka da wani babban laifi bah 
  • Dole ka haye gwajin kwayoyi wato dai sai anma gwaji saboda a tabbatarda baka shaye shaye 
  • Ba aso yazama kanada nakasu a wurin al amrar kuɗi 
  • Ya kasance ɗan shekara 18 zuwa 30 koh kuma 35 ga likitoci da masu magun guna (doctors and pharmacist) kuma kada tsawo yayi kasada 1.65m ga maza 1.60m kuma ga mata 
  • Faɗin ƙirji kada yayi kasa da 0.87 ga maza 
  • Sannan anaso. Yakasance kanada illimin computer kaɗan wannan ba dole bane inkanadashi zaka samu wani amfanin da wanda basudashi barasu samubah 
  • Ka tabbatarda cewa duk wani certificate da kake dashi ka gabatardashi alokacin da ake dubah takardunka domin baza a karɓa bah idan har angama 

Danna Link dake kasa domin yin Apply

Shigo nan domin Cikawa

Allah ya bada sa’a

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!