Abin da ya kamata ku sani kan ƙirƙirar kazar da za ta dinga haifar kaza zalla
‘Yan tsakin da aka jirkita wa ƙwayoyin halitta za su dinga haihuwar kaji ne kawai ban da zakaru
17 Disamba 2022
Masu bincike a Isra’ila sun ce sun ƙirƙiri kazar da aka yi wa ƙwayoyin halittarta kwaskwarima don su dinga haifar kaji mata zalla.
Ci gaban zai iya tseratar da biliyoyin zakaru da ake yankwa a faɗin duniya duk shekara, waɗanda ake ƙararwa saboda ba sa yin ƙwai.
Kajin mata, da kuma ƙwayayen da suke sakawa bayan sun girma, ba sa ɗauke da ƙwayar halittarsu ta asali.
Ƙungiyar kare haƙƙin dabbobi ta Compassion in World Farming ta goyi bayan tsarin.
Dr Yuval Cinnamon na cibiyar Volcani da ke kusa da birnin Tel Aviv, wanda kuma shi ne jagoran shiri n, ya faɗa wa BBC cewa shirin nasu da ya kira “kazar zinare” zai yi matuƙar tasiri kan walwalar kaji.
“Na ji daɗi matuƙa da muka ƙirƙiri wani tsari da zai sauya alƙiblar masana’antar kiwon kaji, na farko dai saboda amfanin kajin da kuma mu kanmu, saboda wannan abu ne da ya shafi kowane mutum a ban ƙasa,” a cewarsa.
Masana kimiyyar sun saka ƙwayoyin halittar DNA da suka kwaskware a jikin kajin waɗanda za su hana duk wani ɗan tayin zakara girma a cikin ƙwan da suka yi. Sabbin ƙwayoyin halittar za su fara aiki ne idan aka haska ƙwayayen a jikin shuɗin haske na tsawon awanni.
Ɗan tayi na kaji mata ba za su samu matsala ba idan aka haska su jikin shuɗin hasken, in ji Dr Cinnamon.
“Masu kiwo za su ga irin kajin da suka saba gani kuma su ma kwastomomi za su samu kajin da suka saba saya a yanzu,” a faɗarsa. “Abin da kawai zai bambanta shi ne za a haska ƙwayayen a shuɗin haske loakcin da ake samar da su.”
Zuwa yanzu tawagar Dr Cinnamon ba ta wallafa rahoton binciken nata ba saboda suna so su samu lasisi ta hannun kamfaninsu mai suna Huminn Poultry, abin da ke nufin sauran masana kimiyya ba su tantance iƙirarin nasu ba.
Amma sun yi aikin ne bisa goyon bayan ƙungiyar kare haƙƙin dabbobi ta Birtaniya wato World Farming (CIWF), wadda ta saka ido kan shirin.
Babban mai bai wa ƙungiyar shawara, Peter Stephenson, ya ce: “Ban fiya son amfani da dabbobin da aka sauya wa ƙwayoyin halitta ba. Amma wannan abu ne na musamman kuma ni da abokan aikina na CIWF mun goyi bayansa,” in ji shi.
“Mataki na gaba mai muhimmanci shi ne mu jira mu ga yadda kazar da kuma ‘ya’yanta da za su dinga yin ƙwai don sayarwa za su isa kasuwa ba tare da ƙorafe-ƙorafen take haƙƙi ba.”
‘Yan tayi maza na mutuwa idan aka haska su da shuɗin haske yayin da suke cikin ƙwai
Yanzu haka akwai ƙudirin doka da ke gaban Majalisar Dokokin Birtaniya, wadda za ta ba da damar yi wa ƙwayoyin halitta kwaskwarima don sayarwa a kasuwa.
Gwamnati na kallon yi wa ƙwayar halitta kwaskwarima wato Gene editing (GE) ya fi karɓuwa a wajen mutane fiye da sauya ƙwayoyin gaba ɗaya wato genetic modification (GM). Ana tsara aikin ƙwayoyin ne a GE, inda a GM kuma ake ƙara ƙwayoyin, wasu lokutan daga wasu halittun.
CIWF ta yi ƙiyasin cewa ana yanka zakaru kusan biliyan bakwai a masana’antun kiwon kaji duk shekara da zarar an haife su saboda ba su da wata riba a kasuwa. Sannan kuma ‘yan kasuwa na ɓata lokaci wajen ware maza da mata bayan ƙyanƙyashe su.
Gwamnatin Jamus ta haramta kashe ‘yan tsaki maza bayan haihuwarsu a farkon shekarar nan.
Ita ma Faransa tana shirin saka irin dokar a farkon shekara mai zuwa.