ABIN MAMAKI ANGO YAFASA AURE A WAJEN DAURIN AURE
Ana gobe zaa daura auran tsohuwar matarsa ya ga ba zai iya jurewa a rasa rai ba, don haka ya samu Wanda zai aureta ya ce masa.
“Ta gaya maka tana da cuta me karya garkuwar jiki kuwa?
Cikin tashin hankali Balarabe ya ce “Cuta me karya garkuwar jiki kuma?
Mahmud ya ce “Eh, a gurin haihuwar yaronmu na biyu aka gano ni da ita muna da wannan cutar, to ina son na gaya maka don na ga alamar ba ka da ita, don na ceci rayuwa, bana son a rasa rai, idan baka yadda ba za ka iya zuwa a muku gwaji, sai anjima.”
Balarabe ya shiga matukar tashin hankali, don haka washegari bayan an cika gurin daurin aure wakilinsa ya tashi tsaye ya ce yana baiwa dangin amarya hakuri domin ango ya fasa wannan aure saboda wasu dalilai, hankalin kowa ya tashi a gurin musamman mahaifinta, guri ya rude da hayaniya da surutai, sai tsohon mijinta Mahmud ya Mike tsaye ya kalli mahaifinta ya ce.
“Baba ni na shirya mayar da auranmu da matata daman sabani ya rabamu har kuka fusata da ni, ina son a kara bani dama “
A take anan mahaifinta ya cika da farin ciki ya ce shi zai biya sadakin ma aka daura aure, bayan an daura aure mahaifin Maryam ya tari wakilan Balarabe ya ce yana son ya gaya masa dalilin fasa auran domin ya san laifin da yarsa ta aikata, wakilin ya gaya masa cewar baya son ya fada cikin mutane ne amma an gayawa Dansu cewar Maryam tana dauke da cuta me Karya Garkuwar jiki, hankalin mahaifin Maryam ya tashi ya shiga gida a fusace.
Maryam da iyayanta mata suna ta jimamin abunda ya faru, Maryam ta ji bakin cikin abun da Balarabe ya yi mata sai dai ta ji dadin yadda tsohon mijinta uban yayanta biyu ya fitar da ita kunya, don haka ta ji ta yafe masa duk wasu kurakurai da ya mata a baya.
Daidai lokacin mahaifinta ya shigo yana mata fada akan boye musu tana dauke da cuta me karya garkuwar jiki har ta so shafawa Wanda bai ji ba bai gani ba, hankalin Maryam ya kara tashi matuka, ta rantsewa mahaifinta bata da wannan ciwo idan kuma bai yadda ba aje a gwada, sai lokacin hankalin mahaifinta ya kwanta.
Cikin bakin rai ta kira Balarabe ta ce sharrin da ya mata Allah ya saka mata, sannan ta gane mijinta na baya shine masoyinta ta kashe waya.
Cikin tashin hankali Balarabe ya je gidansu Maryam a daidai lokacin Mahmud ya zo daukar amaryarsa su wuce.
A fusace Balarabe ya tare Mahmud yana masifar ashe karya ya masa da ya ce Maryam na da cuta me karya garkuwar jiki.
Cikin murmushi Mahmud ya ce “Ka yi hakuri tabbas ban kyauta maka ba, amma kasan na gaya maka bana son a rasa rai ne, to raina za a rasa idan ka auri Maryam, yanzu dai ina son ka yi gaggawar barin kofar gidannan domin gudun fishin hukuma na magana da matar aure.