Yadda Zaku iya amfani da Application biyu a fuskar screen din wayarka

Assalamu Alaikum Barkan mu da sake saduwa a wanan lokacin yan uwa a yau munzo muku da wani sabon Application mai matukar amfani wanda na tabbata zai burgeku sosai matuka
 

Wannan wani sabon Application ne mai suna split Screen zai baka dama ka raba screen din wayarka gida biyu ma’ana zaka iya amfani da Application biyu a fuskar screen din wayarka ta hanyar amfani da wannan sabon Application din a lokaci daya.

HANYAR DA ZAKAYI AMFANI DA WANNAN APPLICATION DIN 

Da farko bayan ka sauke Application din a kan wayarka kana shiga cikin sa zai kawoma yan bayanai na Application saika danna Next bayan ka danna Next zai kawoma fuskar Application din ta asali daga fuskar Application din zakaga inda akasa Enable Service daka gaban Enable service zakaga akwai wata alamar kunnawa da rufewa zaka ganta a rufe to saika kunnata.

zamuyi bayanin abubuwa guda biyu daga cikin wannan Application din wanda zasu baka dama ka iya raba screen din wayarka gida biyu idan kana son amfani da Application biyu a lokaci daya,

Triggers da Floating Button

   
                                 TRIGGERS 

Idan ka duba daga kasa zakaga inda akasa Triggers daka gaban triggers din zakaga akwai wata alamar kunnawa da rufewa zaka ganta a rufe saika kunnata kana dannata kafin ta kunnu zakaga ta kawoma Application da yawa saika duba sunan wannan Application din Split Screen zaka ganshi a rufe saika budeshi kana budewa sai kayi back daga nan idan ka dawo home zakaga Triggers ya budu triggers yana da abubuwa guda biyu Back Button da Home Button

Back Button

back buttom zaka ganshi a rufe saika bude shi amfani nin sa shine idan ka danne Back Button a fuskar wayarka yayin daka shiga cikin wani Application, screen din wayarka zai rabu gida biyu kaga kenan zai baka dama ka sake bude wani a Application din daka kasa ya zama kenan zaka iya amfani da Application biyu a fuskar screen din wayarka a lokacin daya.

Home Button 

home buttom zaga gansu a rufe saika bude su

Amfani sa shine idan ka danne Home Button a fuskar wayarka yayi daka shiga cikin wani Application, screen din wayarka zai rabu gida biyu kaga kenan zai baka dama ka sake bude wani a Application din daka kasa ya zama kenan zaka iya amfani da Application biyu a fuskar screen din wayarka a lokacin daya.

                         FLOATING BUTTON 

Floating Button idan ka shiga cikin sa daka sama zaka ganshi a rufe saika bude shi bayan ka bude shi zai bayyana ma wata alama wanda wannan alamar idan ka shiga cikin wani Application zaka iya dannata ka raba screen din wayarka gida biyu yanda zai baka dama ka sake bude wani Application din daka sa kaga Kenan zaka iya amfani da Application biyu a lokaci daya.

Wannan shine Amfanin Split Screen ina fatan wannan Application ya burgeku,idan wanan application din ya burge ku saiku danna inda nace danna Nan domin yin download

danna nan

Kai tsaye zaka danna gurin da nace ka danna ma’ana Danna nan bayan ka danna kai tsaye zai kaikai playstore. A nan ne zakayi download na Application din

Kai tsaye zaka danna yanda akasa install nan take zaiyi install shikenan saika fara amfani dashi. Na tabbata gai burgeka.

wanan shine ku dai ku cigaba da kasancewa damu a koda yaushe domin samun abubuwa kimiyya da fasaha

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!