An Fara Tantance Wadanda Suka Nemi Aikin Kidaya Na Wucen Gadi Na Shekarar 2023
Assalamu alaikum jama’a barkanmu da wannan lokaci da fatan kowa yana cikin koshin lafiya.
Hukumar kidaya ta kasa ta fitar da bayanan fara tantance enumerators da Supervisors ma’aikatan wucin gadi da hukumar zata dauka domin gudanar da kidayar jamaa na shekarar 2023 an fara tantancewar ne tun daga ranar litinin za a rufe tantancewar ranar 31,ga watan January 2023 a dukkan kananan hukumomi 774 dake najeriya idan har kasan ka nemi aikin kidaya ka ziyarci Sakateriya da abubuwa kamar haka:
- NPC ID slip
- NIN slip
- School Credentials original copies
Idan kuma baka cika ba ka danna Link dake kasa domin Cikawa