Ana sa ran za a samar da Ayyukan yi na wucin gadi 40,000 a cikin jahohi 36 Na Nigeria

Ana sa ran za a samar da Ayyukan yi na wucin gadi 40,000 a cikin jahohi 36 Na Nigeria

Shirin gwamnatin kasar Na (SPW) Special Public Work

kowane mai cin gajiyar shirin zai samun Naira 20,000 duk wata don gudanar da ayyukan gwamnati, in ji karamin ministan kwadago da samar da ayyuka Festus Keyamo a ranar Alhamis.

Za acigaba da kaddamar da aikin tantancewa da kuma tallafawa wadda basa aikin gwamnati da kuma masu kananan karfi karkashi Ma,aikatan horaswa da kuma koyar da sana,a ta kasa baki daya (NDE )wadda akasari take tallafawa masu sana’a.

Ana kuma sa ran shirin zai samar da alawus alawus ga ma’aikata masu tafiya don gudanar da aikin gyaran hanyoyi da gina gidajen jama’a, tsaftar birane da karkara, fadada kiwon lafiya da sauran muhimman ayyuka.

Bankunan za su bude asusu ga duk wadanda suka ci gajiyar shirin kuma a kan haka za su karbi BVN ga wadanda ba su da asusu.

Saboda haka, za a biya duk wasu kudade daga CBN kai tsaye zuwa asusun masu cin gajiyar.

Wannan shiri dai na daya daga cikin manyan tsare-tsare na taimakon al’umma da kowace gwamnati za ta yi cikin kankanin lokaci a tarihin Najeriya.

Haka kuma abin ya sha bamban saboda shi ne tsarin samar da aikin yi kai tsaye na farko na kowace gwamnati da ke tunkarar kasan tattalin arzikin kasa.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!