Gwamnatin Jihar Katsina zata dauki malaman S-Power 7,000 aikin malanta na dindindin

Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana shirinta na daukar karin malaman makaranta 7,000 a fadin jihar. Mataimakin Gwamnan jihar Katsina Hon Faruq Lawal Jobe ya sanar da hakan a lokacin da yake kaddamar da mambobin kwamitin da za su tantance wadanda za a dauka din a ofishinsa, a ranar Juma’a, 7 ga watan Yuli, 2023.

Mataimakin Gwamnan ya ce za a dauki malaman makaranta 5,000 dake da shaidar malanta ta kasa NCE/Diploma da za su koyar a makarantun firamare da kuma 2,000 masu digiri da za su koyar a makarantun sakandare na jihar.

Kazalika, mataimakin Gwamnan ya ce kwamitin zai yi bita kan sabuwar daukar malaman makaranta 3,889 da aka dauka karkashin hukumar kula da ilmin firamare ta SUBEB, inda ya ce za a sake tantance su tare da jarabawa domin tabbatar da ba a yi kitso da kwarkwata ba.

Hon Faruq Lawal Jobe ya yi bayani gamsasshe game da yadda shirin daukar aikin zai kasance.

Tun da farko, Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina Arch Ahmad Musa Dangiwa ya gabatar da mambobin kwamitin da kuma kamfanin kwararri da zai shirya jarabawa ga wadanda za a dauka aikin. Arch Ahmad Musa Dangiwa ya bukaci mambobin kwamitin da su yi aiki tsakani ga Allah ba tare da nuna son rai ba.

Kwamitin dai na da Dr Sabi’u Dahiru a matsayin shugaba sai Malam Lurwanu Haruna Gona a matsayin Sakatare.

Sauran mambobin kwamitin su ne Malam Shamsudden Sani, Dr Isah Idris Zakari, Mannir Ayuba Sullubawa, Shehu Abdullahi Mohammed da Zakariya’u Musa Doka. Kwamitin na da wata daya ya gabatar da rahotonsa.

SSA Isah Miqdad,
Ofishin Daraktan Yada Labarai.
8/7/2023.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!