hanyar da zaka gano wayarka data bata ko aka sace cikin sauki

Assamu Alaikum yan uwa barkan mu da sake saduwa daku a wanan lokacin cikin wannan sabon darasi, a yau inshallahu nazo muku da hanyar da zaka gano wayarka data bata ko aka sace cikin sauki da kwanciyyar hankali.

WANNAN WANI SABON APPLICATION NE

Wannan wani sabon Application ne wanda zaka iya gano wayarka ta hanyar amfani dashi kawai zaka sauke app din akan wayarka kana saita shi koda wayarka ta bata ko ansace ma kana rubuta kalmar location a lambar wayarka ta whatsapp din abokin ka kai tsaye  wannan app din da yake cikin wayar taka da aka sace zai turoma link din da zaka shiga ka gano inda wayarka take ta whatsapp din abokin ka.

YANDA ZAKAYI AMFANI DA WANNAN APPLICATION DIN

Da farko zaka shiga cikin app din kana shiga zai kawoma bayyanan yanda zakayi amfani da application din da yaren turanci saika dinga karantawa kana danna Next bayan fuskar app din ta bude application din zai nemi ka bashi dama ta hanyar danna Allow bayan ka bawa app din daga sama app din zakaga alamar swith ma’ana alamar kunnawa da kashewa saika danna ta danna ta app din zai kawo ma application da yawa yana kawo wa saika duba sunan wannan app din zaka ganshi a rufe saika bude shi kana budewa saika yi back bayan ka dawo fuskar app din daka kasa zakaga inda akasa creat saika danna kana danna wa zai kawama wajan da zakayi rubutu saika rubuta location da karamin baki misali (location) kamar yadda na rubuta amma ka tabbatar L din karko ta fara da karamin baki bayan ka rubuta location din daka kasa zakaga rubutu kala biyu ko wanne da alamar box a farkon sa saika danna tick akan kowacce box bayan nan saika danna Done shikenan ka gama saika app din yanzu idan wayraka ta bata ko aka sace ma kawai kai tsaye zaka ari wayar abokin ka ne ka shiga whatsapp dinsa saika nemi lambarka ka rubta location da L din da karamin baki kamar yadda ka rubuta a farkon bude app din kana rubuta saika danna send kai tsaye wannan app din zai turoma link din da zaka shiga kaga location idan wayarka take kana danna wannan link zai kaika google map sai trackin din yadda wayarka dake cikin sauki da kwanciyar hankali.

IDAN KANA SON DOWNLOAD DIN SA GA LINK NAN A KASA

https://play.google.com/store/apps/details?id=om.roitman.autowhatsapptriggers

Kai tsaye zaka danna link da nace ka danna ma’ana bayan ka danna kai tsaye zai kaikai playstore. A nan ne zakayi download na Application din Kai tsaye zaka danna yanda akasa installing nan take zaiyi install shikenan saika fara amfani dashi. Na tabbata gai burgeka.

KU dai ku cigaba da kasancewa damu a koda yaushe domin samun abubuwa kimiyya da fasaha

mungode 🤝🤝🤝

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!