Ga Wata Dama Ta Samu: Gwamnatin Jihar Kano Zata Bada Scholarship Zuwa Kasashen Waje
Assalamu alaikum warahamatullah barkanmu da sake kasancewa daku a wannan shafin namu mai Albarka.
Gwamnatin jihar kano zata bada scholarship zuwa kasashen wajen a daliban da suke matakin First Class.
Wannan yana daga alqawarurrukan da gwamnatin ta ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓe.
SHARUƊAN DA AKE BUKATA SUNE:
- Ya kasance mai nema cikakken ɗan jihar Kano ne
- Ya kasance ya gama digiri da First Class a jami’ar da take shaidar tantancewa a hukumance.
- Ya kasance mai ƙoshin lafiya
ABUBUWAN DA AKE BUƘATA SUN HADA DA:
- Shaidar zama ɗan jihar Kano
- Takardar haihuwa
- Shaidar gama makarantar firamare
- Shaidar kammala jarabawar sakandare (WASC/GCE/SSCE)
- Shaidar gama digiri mai ɗauke da First Class.
- Transcript da makamantansu
Za’a kai waɗannan takardu ne sakatariyar tantancewa dake tsohon dakin taro na ofishin sakataren Gwamnatin Kano kan titin Wudil Road.
A kula: KADA A WUCE SATI 2 BAA KAI WADANNAN TAKARDU BA.
Akwai website da mai nema zai shiga ya cike bayanan sa domin cikawa danna Apply now dake kasa
Apply Now
Allah ya bada sa’a