Matasa Ga Dama Ta Samu: Bankin UBA Zai Gabatar da Gasa ta National Essay Competition Ga Dalibai Na Secondary School

Assalamu alaikum warahamatullah barkanmu da wannan lokaci da fatan kowa yana cikin koshin lafiya.

Bankin UBA wato uneted bank for africa zai gudanar da gasa mai taken National Essay Competition wanda daliban secondary school zasu gudanar.

Ita de wannan gasa Gasar Rubuce-rubuce ta kasa, wacce ake yi wa manyan daliban sakandare a Najeriya, ana shirya ta ne duk shekara, a matsayin wani bangare na shirin ilimi na UBA Foundation wanda ke da nufin bunkasa al’adun karatu da karfafa gasar lafiya da basira a tsakanin daliban makarantun sakandare a Najeriya da ma Afrika baki daya.

Sharrudan wannan gasar sune kamar haka:

Dole ne ya zama dalibin Babban Sakandare na Najeriya
Dole ne a gabatar da hoton fasfo
Dole ne a gabatar da kwafin hanyar tantancewa (takardar haihuwa, ID na ƙasa, ko fasfo)
Masu nema dole ne su loda kwafin takardun shaidar haihuwa na asali ko shafin bayanan fasfo na duniya.
Masu nema dole ne su loda rubutun da aka rubuta da hannu (bai wuce kalmomi 750 ba) akan tashar.

Abubuwan da Za’a amfana dasu

  • Wanda yayi Na 1st: zai samu N5,000,000
  • Wanda yayi Na 2nd zai samu N3,000,000
  • Wanda yayi N 3nd zai samu N2,500,000

Yadda Zaku Shiga Wannan Gasar ku danna Apply Now dake kasa

Apply Now

Lokacin rufewa: Friday, October 20th, 2023

Allah ya bada sa’a

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!