Nigerian Air Force Sun Sake Bude Shafin Su Domin Daukan Sabin Ma’aikata Na 2023

Assalamu alaikum jama’a barkanmu da wannan lokaci da fatan kowa yana cikin koshin lafiya.

Rundunar sojojin saman Nigeria wato Nigerian AirForce sun sake bude shafinsu domin daukan sabbin Jami’anta na sabuwar shekara

An bude daukan a Ranar 19/12/2022 za a rufe dauka a ranar 30/1/2023

Sunan Aikin da Za a Dauka DSSC Enlistment

DSSC wato Direct Short Service Commission: wani nau’i ne na hukumar a cikin NAF wanda ke buɗe ga farar hula da ma’aikatan soja. Course ɗin yana ba da hanyar yin rajistar masu riƙe digiri waɗanda ƙwararru ne a fagensu. Lokacin horo na wannan nau’in yawanci watanni 6 ne na horon soja mai zurfi kuma ana bawa mutun matsayin Flying Officer.

Abubuwan da ake bukata Wajen Cikawa

  • Dole ka kasance dan Nigeria
  • Shekaru daga 20 zuwa 30
  • Marital Status: duk wanda zai cika ya kasance baida aure
  • Tsayin Namiji: Kar yayi kasa da 1.66 metres
  • Tsayin Mace: Kar yayi kasa da 1.63 metres
  • Medical Fitness: dole mutun ya kasance mai Lafiya
  • Masu Shaidar kammala HND/BSc sune kadai zasu Cika

Domin Cikawa Danna Apply now dake kasa

Apply Now

Bayan ka danna Apply now ya bude zai kawoka shafin saika duba daga kasa zakaga DSSC saika danna kansa sannan ka shiga Start Application

Anan zakaga karin bayani sai kayi kasa ka sake danna Start Application sannan kayi Tick sai kayi continue.

Daga nan zai kawoka inda zaka sanya phone number ka sai kasa sannan sai kayi verify.

Daga nan shikkenan sai kaci gaba da cikawa har kaje karshe bayan ka kammala kayi submit sai kayi print na slip din naka.

Download Nigeria AirForce ShortList

Allah ya bada sa’a

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!