sabon Application wanda zai temaka muku a mu’amalar ku da whatsapp
Assalamu Alaikum warahamatullah. yan uwa barkan mu da sake saduwa daku a cikin wannan sabon darasi a yau nazo muku da wani sabon Application wanda zai temaka muku a mu’amalar ku da whatsapp.
sunana wannan Application din Text Repecter sabon Application ne wanda zai baka dama ka turawa dan uwanka sakon abubuwan ban mamaki a whatsapp Application din yana da bangarori guda bakwai a cikin sa gasu kamar haka
Repected Text
Random Text
Repected Letters
Crazy Text
SACII Emoticons
Blank Text
Emoji Translation
YANDA ZAKAYI AMFANI DA WANNAN APPLICATION DIN
Da farko zamuyi bayanin abubuwa guda bakwai da wannan Application din yake dauke dasu dala dala inshallah sai ku biyu sannu a hankali.
Repected text bangare ne da zaka rubuta kalma sannan a maimaita ma wannan kalmar sau adadin abin da ka rubuta, zaka iya turawa dan uwanka wannan kalmomin da suka maimaita ma ta whatsapp.
MISALI
Ka rubuta hikima tv saika rubuta a maimaita hikima tv sau dari 100.
Random Text bangare ne da zaka rubuta sau nawa za’a maimaita kalma amma ba tare daka rubuta wannan kalmar bar sukuma zasu kawoma duk kalmar da suke bukata shi yasa aka kira wannan bangare da random text.
Repected Text bangare ne da zaka rubuta kalma sannan ka zabi da wanne harafi ko number ko Emoji zasu yima design din wannan kalmar.
Blank Text bangare ne da zaka turawa dan uwanka sako a WhatsApp ko Fecebook ko Instagram ba tare daka rubuta komai ba a cikin sakon
kawai sai dai yaga sako baki babu komai a cikin sa.
Emoji Translation bangare da zaka rubuta kalma su fassara ma wannan kalmar da Emoji
MISALI
(Hello 👋) (Happy 😊)
Crazy Text da SACII Emoticons bangarori ne guda biyu wanda zasu kawoma kalolin Style din rubutu kala daban daban wanda wasu kalolin rubutun ma baka taba ganin su ba kaloli ne na ban mamaki wanda zasuyi matukar burgeka.
IDAN KANA SON DOWNLOAD DINSA GA LINK NAN A KASA
kana danna link din zai kaika playstore a nan zakayi download na Application din.
Bayan Application din ya gama download kai tsaye Application din zai fara install da kansa yana gama wa shikenan saika fara amfani dashi.
KU dai ku cigaba da kasancewa damu a koda yaushe domin samun abubuwa kimiyya da fasaha
mungode