YADDA AKE CHANJA SUNAN WAYA DA KUMA NUMBER VERSION NA WAYAR ANDROID


.
Kamar yadda kuka sani zaku iya chanja sunan wayarku ta android da kuma lambobin version din zuwa duk inda kukeso wato zaku iya chanja sunan wayar taku daga sunanta na Ainishi zuwa wani sunan dabam misali Kana amfani da TECNO to zaka iya mayar da sunanta zuwa GIONEE ko ITEL ko SAMSUNG komade wane irin suna ka gadama zaka iya chanjawa hakanan version zaka iya chanja shi zuwa yadda kakeso misali daga v4.2.2 zaka iya mayar da shi zuwa v4.4.2 ko v5 ko v6 komade wane irin kakeso zaka iya chanjawa,
.
Abin da ake bukata kawai ka tabbatar kayiwa wayarka Root
.
Sannan ka tabbatar kana da ROOT EXPLORE akan wayarka idan baka da ita saika daukota a playstore ko google
.
.
Bayan kayi download dinta saika budeta sannan ka duba folder System saika budeta zakaga wani file mai suna
.
build.prop
.
to abin da zakayi kawai ka danneshi zakaga ya budoma wani shafi saika duba inda aka Rubuta
.
Saika shiga nan idan ya bude zakaga ya nunoma wasu tarkacen code, to karka damu kawai ka nutsu ka duba a hankali zakaga gun da aka Rubuta ro.buid.version.release=4.4.2 to wannan shine version din wayarka amma wata wayar ba =4.4.2 zaka ganiba a a kawai zakaga iya verson din wayar taka to anan saika gogeshi kasa iya version din da kaseso sannan sai kayi kasa ka duba
.
ro.product.model=
.
To anan zakaga sunan wayar taka to sai ka goge ka Rubuta wani sunan da kakeso shikkenan sai kayi back zakaga yayi save kokuma ka danna Menu na wayar ka shiga
.
Save and Exit
.
Shikkenan sai kayi save shikkenan ka gama sai kaje ka kashe wayar taka sanna ka kunnata sai kaje Setting na wayarka ka shiga About Phone zakaga sunan wayarka ya chanja da kuma verson dinta
.
idan kuma zaka dawo da naka na ainishi to saika koma cikin wannan folder System din kaje kan wannan file din mai suna
.
build.prop
.
Sai kayi Rename dinsa zuwa build.prop1
.
Sannan zakaga wani file din mai suna
.
build.prop.bak
.
To sai kayi Rename dinsa ka cire .bak dinnan ka mayar dashi
.
build.prop
.
Shikkenan sai kuyi save sannan ku kashe wayar taku sannan ku kunna
.
Shikkenan kun gama saikuje setting About phone ku duba zakuga ya chanja
.
Asha Shagali lafiya.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!