BABBAN ABINDA KE SA WAYA (PHONE) BATTERY SAURIN TSOTSE CHAJI CIKIN SAURI.

Abinda ke saurin tsotse battery waya.

Duk wanda yake da waya, to kullum zai so ya dinga gyaggyarata wajen dora mata wallpaper Mai kyau da daukar idanu Mai kunshe da kaloli daban daban. But idan muka ga battery na saurin shanye chaji sai muce ay daga inda aka qera tane ba a yi mata battery Mai kyau ba. While ba haka bane matsalar daga yadda muke operating wayar ne

Dalili na farko da kesa battery saurin karewan chaji shine, wallpaper din da muke dora ma wayar mine, kullum cikin neman colourful and bright wallpaper muke don wayar mu ta fito da kyau. Hakan na kashe battery ya zama baya riqe chaji. Don haka abinda yafi shine kawai ka dora wallpaper mai black and white, wato faro da baqi, shine zai sa battery ka ya daina shanye chaji.

Sannan ku daina yawan rike wayanku a hannu idan akwai zafin rana zaisa temperature na wayar yayi high wanda hakan zai sa battery ya sauka cikin sauri, da haka gara kana ajiye wayarka a cikin aljihu ko cikin jaka fiye da yawan rikewa a hannu

Kar ya kasance kana barin notification na Wani app, duk lokacin da zai alerting dinka ya zama sound ne ko vibration, hakan na lalata battery ya zama baya rike chaji.

Don haka duk abinda kasan zai sa battery dinka ya ringa sauka da wuri har daga karshe ya zama ba ya rike chaji to kayi kokari kaga ka cire shi din sama wa battery ka Lafiya da rike chaji

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!