YADDA AKE KWALAKCA

Kwalakca na ɗaya daga cikin abubuwan dake gyara mana jiki, sannan ya sa fatarmu ta yi kyau tare da sa ta ta yi ƙamshi.

Abubuwan buƙata:

  • hawi
  • Misik
  • Farce
  • ambar
  • garin sandal
  • garin kanunfari
  • mahala
  • crem ko loshan
  • madarorin turare kamar kala biyu zuwa uku.

Yadda zamu hada:

Da farko za mu sami mazubi mai tsafta, sai mu ɗauko cream ɗinmu ko loshin, sai mu zuba shi a cikin mazubi da muka tanada. Sai mu kawo garin hawi dinmu, da misalik, da garin farce, da garin ambar, da garin sandal, da garin kanun fari, da malala, duk sai mu zuba su a cikin crem ɗinmu, sai mu yi ta juyawa muna bugawa sai muzuba mu yi ta juyawa har sai mun ga ya haɗe, to daga nan kwalakca ta haɗu.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!