Yadda Zaka Duba Network Na Kowane Banki Kafin Ka Tura Kudi Daga Opay
Assalamu alaikum barkanmu da wananb lokaci da fatan kowa yana cikin koshin lafiya.
Kamar de yadda kuka sani a yanzu opay yana daya daga cikin bank din da ake amfani dashi musamman a yanzu da ake rashin network na sauran banku na.
Hakan yasa opay ya zama kan gaba wajen sharewa masu mu’alama dashi hawaye domin yana basu gudun ma’awa dari bisa dari wajen sauki da kuma saurin tura kudi.
Duk da wannan saurin da yake akwai wasu lokuta idan zaka tura kudi saika tura a wani account din amma sai kudin yaki zuwa, kokuma yaki zuwa akan lokaci.
A yanzu ga wata hanya da zaka duba network na kowane bank da kakeso ka turawa kudi daga opay din. Kafin ka tura kudin saika duba kaga bankin da zaka tura yana da network kokuma bashi idan kaga yana da akwai saika tura idan kuma bashi saika jira ya samu network sannan saika tura.
Ga yadda zakayi:
Da farko ka danna Link dinnan domin saukar da Application na opay business
Download Opay Bussiness
Bayan kayi download sai kayi install dinsa sannan saika bude shi bayan ka bude sai kayi login na opay din naka, wato kasa number wayar ka da kuma password dinka bayan kasa zai budema cikin ca, saika duba inda aka rubuta More saika shiga
Bayan ka shiga nan saika duba inda aka rubuta Network saika shiga wajen:
Idan ka shiga network bayan ya bude zai nunama Withdraw da kuma Deposit saika duba wanda zakayi idan transfer zakayi saika shiga deposit anan zakaga jerin bankuna:
Tare da Parchent na kowane bank saika duba kagani idan bank din da zaka tura kudin yana da network saika tura, idan kuma bashi da network saika jira ya dan hau sannan saika tura kudin.
Allah ya bada sa’a