Yadda Zaka Gano Tsawon Lokacin Daka Dauka Kana Amfani Da Wayar Ka
Assalamu alaikum warahamatullah barkanmu da sake kasancewa daku a wannan shafin namu mai Albarka da fatan kowa yana cikin koshin lafiya.
Yau zanyi bayani akan yadda zaku gano tsawon lokacin da kuka dauka kuna ta amfani da wayar ku, tare da tsawon lokacin da kuka dauka a cikin kowane application da kuke amfani dashi a wayar ku.
Wanann hanya tana aiki ne a wayar android ban saniba ko iphone ma nayi amma de a wayar android na gwada itama iphone may be akwai nata hanyar dabam.
Da farko ka shiga setting na wayarka
Bayan ka shiga sai kayi kasa ka duba inda aka Rubuta Digital wellbeing & parentel contrals
Da zarar ya bude anan zakaga dukkan tsawon lokacin daka dauka kana amfani da wayar ka, tare da sunayen wajajen daka shiga da kuma lokutan dakayi kana amfani a inda ka shiga
Wannan shine hanyar da zakasan lokutan da kake batawa kana amfani da wayar ka.
Idan ka gani yana dakyau ka tsaya ka lissafa ka gani shin kana bata lokutanne a banza kokuma kana amfani dasu ta hanyar daya dace.
Allah yasa mu dace