Yadda Zaka Kulle Chat Dinka Na Whatsapp Idan Bakaso Wani Ya Gani

Assalamu alaikum barkanmu da wannan lokaci da fatan kowa yana cikin koshin lafiya.

Ina wadanda basason wani yaga wani chat dinsu misali idan kana da budurwa kanaso ka kulle chat dinka domin kar wata budurwar taka ta gani ko makamancin haka.

Da farko idan whatsapp din ka ba updater bane kaje kayi update dinsa.

Yanzu saika shiga whatsapp dinka bayan ka shiga sai kaje kan wanda kakeso ka kulle chat din naku saika bude

Saika danna Kan DP dinsa

Bayan ka danna idan ya bude saika duba daga kasa zakaga Chat Lock saika shiga

Bayan ya bude zaka ganshi a rufe saika budeshi

Daga nan zai nunoma ka sanya thumbprint dinka saika sanya

Idan kayi haka shikkenan ka kulle chat dinka da wanann mutumin babu wanda zai gani

Idan kanaso ka kaga chat din naka saika duba daga home na whatsapp din naka zakaga chat lock saika dannan anan zakaga wanda ka kulle chat din saika shiga ka bude kokuma kuyi chat din.

Allah ya bada Sa’a

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!