Yadda Zakayi Apply Na Nigerian Immagration Service
Da farko ka shiga wannan link din 👇 https://cdcfib.career/ kana shiga zai kaika shafin nasu da zaka gani kamar haka
Toh saika taba kan Apply Now inda zaikaika shafin kamar haka, sannan kamaida browser desktop site idan a waya kakeyi yadda zaka maida browser naka desktop site shine ka dubah saman chrome browser dinka zakaga wasu ɗigo ƙwaya uku ta gefen dama saika taba kansu zasu baka wasu options a ciki ka dubah zakaga inda akasa Desktop site saika taɓa shikenan
Toh anan kaza buɗe profile ne saika lura da kyau ka cike komai daidai wurin da zaka zaɓi categories kuma yanada kyau ka tsaya ka karanta kowanne categories kafun ka fara zaba sannan zurin password shima dole saikasa password mai ƙarfi kamar haka Howgist123@@@ saikayi save and continue shikenan ka buɗe profile ɗinka , daganan zaikaika shafin da zakasa person details dinka wato bayanai akan kanka sannan zai baka application code kamar yadda zaku gani a photon dake kasa
Toh saika ɗau Application code ɗin naka koda network ya baka problem zaka dawo ka cike abunka, kana gamawa saika danna kan save and continue zaikaika wurin sakah passport photo kenan koh ya kaika wurin primary school information saika sa wannan bayaninna makarantanka sunanta da shekarar da ka shiga da kuma wadda ka gama sai certificate shine FSLC wato first school leaving certificate saika danna kan save and continue zaikaika wurin na secondary school information naka kamar haka
Toh saika shima kamar yadda kasa na primary school ɗinka saika danna kan save and continue zai buƙaci da ka upload na results dinka kamar haka
Saika dannan inda akasa add NECO results kana dannawa zaikaka shafin da zaka ɗaura results dinka ba dole saika daura dukka 9 bah koh da guda biyar kasa yayi Kamar yadda zaku gani a photon dake kasa
Kana gama ɗaurawa saika taba kan done shikenan ka gama da wannan idan na masu secondary school kake cikewa shikenan saika duba sama inda aka rubuta passport photograph saika taba zai kaika inda zaka upload na photon ka shima kada ya wuce 80kb zaka iya rageshi ta hanyar amafani da photo resizer
Kana gama upload nashi shikenan inkuma kayi tun a farko toh basaika sakeh bah zai nunama shi a summary inka kamar haka
Saika dubah duk abunda kasa daidaine idan daidaine saika submit nashi shikenan ka gama. Saikayi download nashi a PDF kaje ama printing nashi a cafe.
Allah ya bada sa a
A.I.H
©Arewatech360