Sabuwar Hanyar Da Zaka Dora Whatsapp Dinka A Wayoyi Guda Hudu 4

Assalamu alaikum warahmatullah wa barakatuh ‘yan uwa barkanmu da yau barka da kasancewa da SIRRIN ANDROID.

A rubutun namu na yau zanyi cikakken bayani ne dangane da feature da whatsapp suka fito dashi kwanan nan.

A kwannan nan kamfanin whatsapp suka fito da wannan tsarin da zaka iya daura whatsapp dinka a wayoyi fiye da daya, to amma mafi yawan mu yadda muke tunanin feature din ba haka yake ba, ba wai zakayi register a wayoyin fiye da daya bane, zakayi LINKED na tsohon account dinka ne a wayoyin, kuma zaka iya saukewa a duk lokacin da kakeso.

Cikakken bayanin yadda ake linked din


Da farko zaka shiga tsohon whatsapp dinka zaka danna ɗigo 3 da nayiwa arrow a photon fari, bayan ka danna sai ka shiga inda aka rubuta “LINKED DEVICES” bayan ya buɗe sai ka shiga inda aka rubuta “LINK DEVICE” zai nunama camera inda zakayi scaning kamar irin wanda akeyi a xender idan za’a tura wani abu.

A wayar da kakeso kayi linked whatsapp ɗin kuma zaka sauke sabon whatsapp ne bayan ya bude ko ka tura ta xender, bayan ka bude whatsapp din ya nunama inda zaka shigar da number kada ka shigar da numban, ka duba daga sama zakaga ɗigo 3 sai ka danna su, zakaga “LINKED TO EXISTING ACCOUNT” sai ka danna gun, zai nunama QR da zakayi scanning already a tsohuwar wayar ya kaika inda da zakayi scanning sai kawai kayi scanning kamar yadda akeyi a xender idan za’a tura wani abu, sai ka jira ‘yan sakanni nan take zakaga ya hau kan sabuwar wayar.

NOTE: Ba zaka iya amfani da su lokaci daya ba.

Allah yasa mu dace

©Sirrin Android

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!