YADDA ZAKU RINKA TURA SAKON MESSAGE KYAUTA A KOWANI LAYI

Assalamu Alaikum barkan mu da wannan lokaci sannun mu kuma da sake kasancewa daku a dai-dai wannan lokaci.

To kamar yadda kuka gani a title na wannan rubutun shine yadda mutum zai na tura sakon message kyauta a kowanda layi insha Allah yau zamu koyar da wannan darasin.

Dan haka ka tsaya ka karanta wannan darasin tun daga farkon sa har karshe hakan ne zai baka damar gane abinda muke nufi da kuma yadda zakana tura sakon kyauta.

Amma kafin muje cikin darasin namu zanso kataba alamar subscribe da take futowa daga kasan website dinnan kana tabata shikenan a duk lokacin da mukazo da sabon darasi zaka sameshi kai tsaye a notification na wayar ka ana mai sanar dakai munyi sabon posting nasan zaka taimaka ka danna alamar allow din nan domin karuwa da wannan website mai Albarka, tunda ka dannan bara mushiga cikin darasin kai tsaye.

Nasan tabbas wasu zasuyi mamaki jin sunji munce yadda mutum zai na tura sakon message kyauta ga kowa da kowa da kakeso katurawa sako kuma a kowanda layi.

To zamuyi amfani da wata hanya ne ta Application wacce da’ita ne zaka samu damar tura sakon kyauta ga kowanda layi, dan haka yanzu batare dana cikamu da surutu ba kai tsaye mutum yaje ya danna inda akasa Danna Nan a karshen rubutun nan namu domin ya dauko Application din.

Bayan kadauko Application din kai tsaye zaka budeshi kana budeshi zai ce ka zabi yaren da kakeso kayi amafani da Application din saika zabi wanda kakeso amma inaga ka zabi English dan zaifi maka da din koyo, bayan ka zabi english zai tafi dakai wajen da zakayi register da wannan Application din sai ka ciccike duk bayanan da kaga an tambayeka nayin register.

Amma a kula yayin register ka tabbatar layin da zakayi register dashi yana kan waya kuma yana kusa dakai, domin za’a turoma Otp-Code da zaka sanya yayin da kakeyin register.

Bayan ka kammala register gaba daya kai tsaye zai shigar dakai cikin Application din inda zakaga Application din tamkar chatting yake asalima zan’iya ce muku chatting ake dashi, anayin chatting dashi mutum ya zama friend din ka kuna chatting sosai da sosai kamar WhatsApp.

Amma ana iya tura sako kai tsaye yajewa mutum ta cikin message din sa wanda shi wannan its free zaka iya turawa kowa sakon yaje masa kuma yagani ta cikin message din sa, kuma kyauta zaka tura.

Dan haka bayan kayi register ya nuno maka fuskar wannan Application din akwai messages da zaka samu guda daya tilo wanda zaka ganshi daga kampanin da suka kirkiri Application din ne, dan haka sai ka bude wannan message din kana budewa zai baka dama kuyi magana da mutanen su domin su taimaka maka wajen yin amfani da Application din akan duk abinda ya shigema duhu kaga baka sani ba da zarar ka tambayesu zasu baka amsar yadda zakayi.

Amma kada kuce ban koya muku yadda zaku na tura sakon message din ga kowa ba, ga yadda zakuyi

Bayan kayi register ya kawo ka fuskar farko ta Application din ka kula daga kasa zakaga alamar + ta fito kama ta whatsapp sai ka tabata kana tabata zata kai ka inda zakaga duka contact na wayar ka, anan ne zaka zabi duk wanda kakeso katurawa sakon message kawai sai ka taba sunan mutum kaje ka rubuta masa abinda kakeso ka rubuta masa shikenan sai ka danna sending take message din zai tafi, kuma shi wanda ka turawa zai ga sakon message din yaje masa ta gurin message din sa, ya karanta yadawo maka da replay.

Sannan a gurin contact din naka daka shiga duk wanda ya tabayin register da wannan Application din zaka ganshi an nunama shi, to wannan shine wanda zaku iyayin chatting dashi tamkar a whatsapp direct ta cikin Application din.

Anan zamu dakata kada naja rubutun namu dayawa, akwai abubuwa da dama da wannan Application din yakeyi na free zamuna zuwa dasu daya bayan daya muna koya muku insha Allah, duk dama duk wanda ya bude Application din ma’ana yayi register dasu zai fahimci Application din sosai domin Application din yanada saukin koyo.

Amma inaso kowa yasani cewa wannan Application din baya amafani sai ka bude data, wannan shine. Ga application dinnan a kasa?

Download App

Mungode da kasancewa da Howgist.com

Dan Allah kada a manta wajen yin share domin ‘yan uwa sugani su amfana.

Sai kunjimu a darasi na gaba.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Check Also
Close
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!