YANDA ZAKA BIYI LAMBAR WAYAR MUTUM KA GANO INDA YAKE

Assalamu Alaikum warahamatullah. yan uwa barkan mu da sake saduwa daku a cikin wannan sabon darasi a yau nazo muku da wata hanyar mai matukar amfani hanya ce da zaka iya gano mutum ta lambar wayarsa.

YANDA ZAKA BIYI LAMBAR WAYAR MUTUM KA GANO INDA YAKE 

Wannan wata sabuwar hanyace wacce da whatsapp suka futo da ita (Live Location) kamar yanda kuka sani yanzu lokaci ya chanja ana yawan fata da matsalar satar mutane da kuma matsalar Kidnapping yanzu idan wani dan uwanka zaiyi tafiya mai nisa zaka bashi shawara ya shiga whatsapp dinsa ya turoma da Location din tafiyar da zaiyi domin ka dinga lura da tafiyar tashi kai kuma wanda ya turowa da location din ta wannan Location din daya turoma idan ka shiga zaka iya bibiyar sa ka gano inda yake kaga wannan hanyar ce mai matukar amfani.

HANYOYIN DA ZAKA BI IDAN KANA SO GANO INDA MUTUM YAKE 

Da farko idan kai matafiyi ne zakayi tafiyar mai nisa zakayi tafiya ne da kano zuwa Abuja ko daga Kaduna zuwa Legas kaza shiga Whatsapp dinka ka nemi lambar wani dan uwanka wanda ka aminta dashi wanda bazai cutar dakai ba saika shiga kan lambar sa kana shiga daka kasa wajan da ake typing ma’ana rubutu daka gefen Camera zakaga wata alamar a kanan nade saika danna ta kana danna ta zata kawo ma zabi guda shida saika nemi zabin da aka rubuta (Location) saika danna kana danna wa zai kawo idan zaka turawa dan uwanka location din tafiyar da zakayi daka sama zakaga inda aka rubuta (Share Live Location) saika danna kana danna wa zai kawoma ka zabi adadin Lokacin da wannan Location din daka tura zaiyi aiki.

MISALI

Idan zakayi tafiya daka Kano zuwa Kaduna idan tafiyar zaka dauke ka awa daya akwai idan akasa 1 hours saika danna kaga Kenan wanda ka turawa da Location din tafiyar da zakayi zai dinga bibiyar tafiyar ka tun daga lokacin daka tashi har zuwa lokacin da zaka sauka.

Idan kuma tafiyar da zakayi daka Kano ne zuwa Legas  idan tafiyar zata dauke ka awa takwas akwai idan akasa 8 hours saika danna kaga shima Kenan wanda ka turawa da wannan Location din tafiyar da zakayi zai dinga bibiyar tafiyar taka tun daga lokacin daka tashi zuwa lokacin da zaka sauka.

Bayan ka zabi adadin Lokacin da zaka ci a wannan tafiyar taka saika danna kana danna wa daka kasa zakaga inda akasa (Add Comment) ma’ana ka dan yiwa wanda zaka turawa da Location din tafiyar da zakayi wani dan jawabi 

MISALI

Aisha dan Allah zan danyi tafiya ne daka Kano zuwa Kaduna zamu tashi yanzu a mota gashinan na turoma Location din tafiyar da zanyi dan Allah ka dinga lura da tafiyyar tamu sabuda yanayi na rayuwa.

Bayan ka gama rubuta masa dukkanin jawabin tafiyar taka idan ka duba daga gefe zakaga alamar Send saika danna kana dawa shikenan ka turamasa Location din tafiyar da zakayi.

Shi kuma dan uwan naka yana shiga Whatsapp dinsa zaiga wannan jawabin dakai masa tare Location din daka turamasa shi kuma lokaci bayan lokaci zai dinga shiga wannan Location din daka turamasa yana bibiyar tafiyar taka har saika sauka lafiya.

Ba fata ake ba idan kuma kaga da wata matsala a Location din Location din ya tsaya a gurin da bai kamata ace ya tsaya ba kuma ka kira lambar wayarsa a rufe sai kayi gaggawa sanar da police domin suma su sake bibiya.

Wannan babbar hanya ce da zata temaka wajan rage sace sace mutane da kuma kidnapping.

wanan shine ku dai ku cigaba da kasancewa damu a koda yaushe domin samun abubuwa kimiyya da fasaha

mungode

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!