Yanda Zaku Karanta Message Din Da Aka Goge A Whatsapp

Assalamu Alaikum warahamatullah. yan uwa barkan mu da sake saduwa daku a cikin wannan sabon darasi a yau nazo muku da wani muhimmin Applications mai matukar amfani.  

sunan wannan Application din Recover Deleted messages wannan sabon Application din zai tema kama wajan dawo da dukkanin messages din da aka turoma a WhatsApp wanda aka goge shi kafin ka gani irin wannan matsalar na faruwa zakaga kuna cikin chat da mutum ya turoma message kafin ka gani ya goge shi to idan har kana son ganin wannan message din daya turoma ya goge shi kafin kagani zakayi amfani da wannan Application din.

YANDA ZAKA SAITA WANNAN APPLICATION DIN 

Da farko kana shiga cikin wannan Application din zai kawo ma dokokin sa tare da tsare tsaren sa sai ka nutsu ka karanta su kana gama karantawa idan ka yadda da abin da App din yazo dashi saika danna alamar Good dake kasa kana danna wa zai kawo ma wasu abubuwa dukkanin su zaka gansu a rufe saika bude su kana bude su shikenan ka gama saita wannan Application din.

HANYAR DA ZAKAYI AMFANI DA WANNAN APPLICATION DIN 

bayan ka gama saita wannan App din amma kafin ka shiga cikin wannan Application din sai irin wannan matsalar ta faru dakai wani ya turoma message kafin ka gani ya gogeshi, idan ka shiga cikin WhatsApp dinka kaga an turoma message an gogeshi baka gani ba kuma kana son ganin wannan message din zaka shiga cikin wannan Application din mai suna Recover Deleted messages dama already kana dashi a cikin wayarka kana shiga zakaga ya kawo zabi guda biyu Nomal WhatsApp da Business WhatsApp saika zabi WhatsApp din da kake amfani dashi ka danna inda akasa Deleted message kana shiga shima zakaga ya kawo zabi guda biyu Deleted messages da Deleted media idan message aka turoma sannan aka goge shi kafin ka gani zaka shiga inda akasa Deleted messages kana shiga zakaga wannan abin daka turoma sannan aka goge shi kafin kagani idan kuma hoto ko video ko recording aka turoma sannan aka goge shi kafin kagani saika shiga Deleted media kana shiga shima zakaga wannan abin daka turoma sannan aka goge shi kafin kagani.

IDAN KANA SON DOWNLOAD DINSA

Danna nan
 

Kai tsaye zaka danna gurin da nace ka danna ma’ana Danna nan bayan ka danna kai tsaye zai kaikai playstore. A nan ne zakayi download na Application din.

Kai tsaye zaka danna yanda akasa install nan take zaiyi install shikenan saika fara amfani dashi. Na tabbata gai burgeka.

KU dai ku cigaba da kasancewa damu a koda yaushe domin samun abubuwa kimiyya da fasaha

mungode ???

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!