Ƙwalejin ATAP za ta fara ƙwasa-ƙwasan PGD a shekarar 2023

Ƙwalejin Kimiyya da Fasaha ta Abubakar Tatari Ali dake Bauchi za ta fara ƙwasa-ƙwasan share fage wato PGD a bangaren tsaro da nazarin dakile ta’addanci a wani matakin bunƙasa harkar ilimi a jihar Bauchi.

Shugaban tsangayar gama garin ƙwasa-ƙwasai wato School of General Studies a turance, Dr. Muhammad Auwal Sulaiman, shine ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a wurin rufe taron ƙarawa juna sani na tsawon kwana 5 kan matsalar tsaro da kuma tattaunawa da ƙwararru a fannin.

Dr. Muhammad yace ilimi ginshiƙin rayuwa ne hakan ne yasa ƙwalejin ke huɓɓasawa kan wannan bangare kamar yadda yake a tsarin shugaban makarantar wajen ganin an samar da sabbin ƙwasa-ƙwasai.

Ya kara da cewa, Ƙwalejin ta hada hannu da sauran manyan makarantu domin samar da sabbin darussan makarantu wa ɗalibai domin yin gogaiya da taƙwarorinta a fadin ƙasar nan.

Shima da yake a lokacin taron, Ko-odinetan Hukumar Samar da Cigaban Yankin Arewa Maso Gabas ta NEDC reshen jihar Borno, Engr. Mohammed Umaru ya fayyace irin yadda hukumar su ke taimakon al’umma musamman a bangaren karatu da sha’anin tsaro.

Engr. Umaru sai ya yabawa ko-odinetan taron inda yace samun mutum kamar sa cikin al’umma abune mai wuya.

Taron dai da ya ƙunshi tattara ƙwararru a fannin tsaro musamman masu zaman kansu domin tattauna hanyoyin magance tsaro a yankin, ya samu mahalarta daga jihohin arewa maso gabas in da kuma suka jinjina wa ƙwalejin ATAP da Hukumar NEDC bisa wannan yunkuri.

An gudanar da taron dai, a dukkan jihohin Arewa Maso Gabas, da aka kammala a Jihar Borno kuma na karshe a shekarar Bana inda kuma Mal. Musa Yakubu Sallau da Mal. Faruk Aliyu na ƙwalejin ATAP suke gabatar da maƙalu a dukkan tarukan.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!