ABUBUWA 10 DA ZASU INGANTA ZAMAN AURENKI
Abubuwa 10 Da Zasu Inganta Zaman Aurenki:
1: Kada ki shigo da karyan rashin lafiya domin hana mijinki Jima’i.
2: Kada ki rika daga muryarki sama dana mijinki idan kun samu matsala.
3: Kada ki bayyana sirrin mijinki ga ‘yan uwanki ko kawayenki.
4: Kada ki kaskantar da mijinki saboda kin fishi samu ko daukaka.
5: Kada ki rika kwatanta wasu mazan da mijinki saboda ya gaza a wani fanni.
6: Kada ki barwa ‘yar aikin ki aiyukan da ya kamata ke zaki yiwa mijinki.
7: Kada ki bari wata ta samu kusanci da mijinki saboda gazawarki a wani fanni.
8: Kada ki yi mu’amala da matan da basu daraja zaman aure.
9: Kada ki zama mace mara godiya wajen mijinta
10: Kada ki musgunawa ‘ya’yan mijinki da suke gabanki.