Garabasa: Yadda Zaku Sayi 450MB A N120 ko 200MB A N60 kokuma 15GB A N3000 da 45GB A N6000 A Layin MTN
Assalamu alaikum jama’a barkanmu da wannan lokaci da fatan kowa yana cikin koshin lafiya
A yau nazo muku da wani tsari a layin mtn wanda zai baku damar dayan data mai dan sauki musamman a wannan lokaci.
Dan haka idan kana bukatar dayan data mai sauki a layin mtn ba tare da sai kana cikin wani tsari na daban ba to wannan damar takace domin akowane tsari kake wannan hanyar zaka iya sayan wannan datan.
Wato zaka iya sayan 450MB A N120 ko 200MB A N60 kokuma 15GB A N3000 da 45GB A N6000
Sunan wannan tsarin ALWAY ON PLANs
Yadda tsarin yake shine da zarar ka shiga cikinsa ka sayi datan shikkenan kullum akwai adadin datan da zasuna baka domin kayi amfani da ita,
Misali ka sayi 15GB akan N3000, kullum zasuna tura maka 500mb kaga kenan idan anyi kwana 30 kaci 15gb, sannan wani abun burgewa da wannan tsarin shine, idab aka turoma adadin mb din da zakayi amfani da ita a ranar, sai kuma bala karar da itana, zasu adana maka datan ka wanda bayan tsarin daka shiga ya cika kwanakin daka saya, ma’ana datan yayi expire, to idan ka sake saya zasu dora maka akan waccem wadda tayi expire baka karar da itaba zatayi aiki.
Dan haka ga yadda zaku shiga cikin tsarin.
Da farko ka danna *131*1# daga nan zai kawo maka zabi sai kayi Replay da Number 5 anan take zai nuna maka jerin datan kamar yadda na lissafo a baya, saika duba ka sayi wacce tayi maka.
Allah ya bada sa’a