ABUBUWA 12 DA MATA SUKA TSANA A LOKACIN JIMA’I
Sau tari, maza magidanta sukan yi wasu abubuwan da matansu suka tsana ko suke ki a yayin da suke gudanar da jima’i, sai dai kuma kadan ne daga cikin matan sukan iya fitowa fili su nunawa mazajen nasu rashin jin dadinsu ga irin wadannan dabi’on ko halayen.
Ire-ire wadannan halayen na wasu mazan yakan kuntatawa mata, hakan kuma yakan yi sanadiyar samar masu da rashin gamsuwa a lokuta da dama yayi gudanar da jima’i da mazajensu.
Ga jerin wasu abubuwan 12 da mata suka tsana kamin, lokaci da kuma bayan kammala jima’i.
1-Rashin Tsafta- Wasu mazan basu iya tsaftace jikinsu kamin su tinkari matansu da jima’i. Ana samun wasu mazanma a lokacin da suka shiga wanka basa kula da mahimman wuraren da ya kamata su tsaftacesu da kyau ganin mahimmancin su a lokacin gudanar da jima’i.
Wurare irin su baki, hamata, matsaimatsi, da kuma ‘ya’yan maraina, wurarene da mata suke matukar son ji da ganinsu a tsaftace a duk
lokacin da mazansu suka tinkaro su a jima’ince. Don haka rashin tsaftacesu, yakan hana mace samun jindadi kamin da kuma lokacin gudanar da jima’i.
2-Wasanni Motsa Sha’awa- Wasu mazan sam basu da al’adar motsawa matansu sha’awarsu ta jima’i ta hanyar wasannin motsa sha’awa, yadda zai sa mace sha’awarta ya matsa sosai ta kuma ji ta kamu da bukatar mijinta. Mata da dama sun koka ta yadda mazansu da sun tashi gudanar da jima’i dasu sai dai kawai su musu hawan kawara ba tare da motsa musu sha’awa ba, wanda hakan yasa mata da suke fuskantar irin wannan matsalar suke tsanar yin jima’i a lokuta da dama. Mata suna sha’awar ayi musu wasanni da dama kamin a soma gudanar da jima’i dasu.
3-Rashin Maida Hankali- Mata sun tsani a lokacin da za a soma ko ake jima’i dasu hankalin namiji ya koma wani wajen. Mace na bukatar ganin mijinta ya tattara hankalinsa gaba daya a kanta kamin, lokacin ko bayan kammala jima’i da ita. Don haka ne mata suka tsani namiji yana amsa waya ko kallon talabijin, ko kuma yin wani batun da bashi da alaka da abunda suke gudanarwa a wannan lokacin. Dole muddin namiji yana son ganin ya gamsar da matarsa, to ya maida hankalinsa gaba daya a kanta a yayin da yake tare da ita.
4-Lokacin Yin Jima’i- Kashi 80 cikin 100 na mata sunfi sha’awar a yi jima’i dasu ne a lokaci da suke da sha’awar yi ba a lokacin da basu da sha’awa ba. Mata sun tsani namiji ya tilastasu yin jima’i ba tare da suna da bukatar yin shi ba a wannan lokacin. Don haka yana da kyau maza suyi la’akari da lokacin da mace take sha’awar jin jima’i da kanta, domin ta hakan ne maigida zai iya samun biyan bukatar da za a sakar masa jiki sosai domin akwai wasu lokutan da mace batada sha’awar jima’i a rayuwanta.
5-Yanayin Kwanciya- Duk mace tana son mijinta ya sadu da ita da yanayin da yafi mata dadi kuma yake da sauki da saurin gamsar da ita. Mata sun tsani mazajensu su kwanta dasu a yanayin da basu jin dadinsa wanda hakan yake sa mace ta tsani gudanar da jima’in ko kuma ta kasa samun gamsuwa. Don haka yana da kyau maza su kula kuma suyi la’akari da yanayin kwanciyar da mace ta tsana da kuma wanda tafi sha’awa a yayin jima’i.
6- Sauke nauyinka a kanta- Maza musamman masu nauyin jiki, sukan cutar da matansu a lokacin da suka sauke nauyinsu akansu a yayin gudanar da jima’i. Hakan na hana macen ta samu sararin sarrafa jikinta yadda take bukata. Maza masu tunbi ko girman jiki su rika amfani ne da yanayin kwanciyar jima’in da bazai takura matansu ba.
7- Saurin Zuwan Kai- Dukkannin mata sun tsani mazansu suyi zuwan kai da wuri a yayin gudanar da jima’i, wanda hakan yana matukar cutar da mace a rauyuwarta, don haka wasu matan suka gwammace zama da rashin jima’i maimakon yin jima’in da namiji mai saurin zuwa. Dole ne maza masu irin wannan matsalar suyi kokarin ganin likita domin samo magani.
8- Yin Shuru- Mata suna son jin namiji yana sumbatu a lokacin da yake saduwa dasu.Mata sun tsani mazansu na saduwa dasu
suna gum da baki tamkar kurma. Don haka yin sumbatu a yayin jima’i da mace, yana kara mata kwarin gwiwa dama gamsar da ita a wasu lokutan.
9-Rashin Alamta Zuwan kai- Mata sun tsani mazansu suyi zuwan kai ba tare da sunyi musu wata inkiyar da zata nuna masu cewa suna kan hanyar zuwa ba. Alamta zuwan kai wajen namiji a yayin saduwa da matarsa itama yana kara mata wani jin dadin. Yana da kyau namiji ya nuna wani alamin a lokacin da yake kan hanyar zuwa da kuma bayan zuwar tasa.
10- Saurin Tashi- Mata sun tsani namiji da zaran ya biya bukatarsa yayi saurin tashi daga jikinta. Mace tana bukatar tabbatar da cewa namiji yana tare da ita koma yana jikinta bayan ya biya tasa bukatar. Domin a wannan yanayin tana iya samun gamsuwa idan mai gida ya rigata.
11- Zuwan kai a waje- Mata sun tsani namiji yayi zuwan kai a wajen farjinsu ba a cikinsa sai dai idan ita ce ta bukaci yin hakan saboda wasu dalilai.
12- Rashin Sadarwan Jima”I- Maza da dama basu da al’adar yin sadarwan jima’i da matayensu kamin, lokaci da kuma bayan kamala kwanciya irin na jima’i. Yana da kyau kasan abunda matarka takeso ko ta tsana a lokacin gudanar da jima’i. Wannan tattaunawar zai baiwa mace daman bayyana maka abubuwan da ke mata dadi a lokacin wasannin motsa sha’awa, lokacin gudanar da jima’i da bayan kammala shi domin ka kaucewa abunda bata so ka kuma inganta abunda take so.