Application din zai taimaka maku sosai gurin lissafa abubuwa masu yawa a Lokaci Daya

Assalamu Alaikum Barkan mu da sake saduwa daku a wanan lokacin sake saduwa a yau zamuyi bayani ne akan wani babban Application wanda na tabbata zai temaka muku a mu’amalar ku da wayoyin ku na yau da kullum. 

AMFANIN WANNAN APPLICATION DIN 

Sunan wannan Application din (Count things) Application ne wanda fiye da mutum miliyan daya ne suke amfani dashi, kaima kar ka bari a barka a baya na tabbata zai burgeka.

Wannan Application din zai taimaka maka sosai gurin lissafa abubuwa masu yawa, misali idan kana da katako da bulo masu yawa ko kuma wani abun mai yawa wanda kake son irga shi a lokaci daya, wannan Application din zai irga maka su cikin sauki da kanciyar hankali.

HANYAR DA ZAKAYI AMFANI DA WANNAN APPLICATION DIN

Da farko bayan ka sauke Application din akan wayarka zaka shiga cikin sa daka kasa zaka ga inda akasa Countinue zaka ga yana kawo ma short video na yanda zaka yi amfani da Application din kana danna continue yana kara kawoma short video na yanda ake yin amfani da Application din har fuskar Application din ta bude bayan fuskar App din ta bude daka kasa zaka wata alamar Camera saika danna ta zasu baka zabi biyu idan abinda kakeso wannan Application din ya irga a lokacin zaka dauki hoton sa zaka danna Camera idan kuma kana da hoton abinda kakeso a irga saika danna gallery ka dakko shi bayan ka dakko hoton saika danna Count kai tsaye zai irga ma adadin abinda kasa. 

IDAN KANA SON DOWNLOAD DINSA GA LINK NAN A KASA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.countthis.count.things.counting.template.counter

bayan ka danna kai tsaye zai kaikai playstore. A nan ne zakayi download na Application din

Kai tsaye zaka danna yanda akasa install nan take zaiyi install shikenan saika fara amfani dashi. Na tabbata gai burgeka.

KU dai ku cigaba da kasancewa damu a koda yaushe domin samun abubuwa kimiyya da fasaha mungode 🤝🤝 🤝

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!