YADDA MATSALAR AURE KE FARAWA

A lokacin farko da miji ya gamu da matar shi, ita ce macen da tafi kowacce mace kyau a duniya. Yakan kirata da sunaye kamar: Baby, queen, darling, sweetheart, end of discussion, sarauniyyar kyau da dai sauransu…

Da zarar anyi aure, rayuwa tana tafiya dai-dai saboda ma’auratan suna son junansu…

Ana cikin tafiya sai macen tayi ciki, kamanninta su canja daga sarauniyyar kyau zuwa wani abun daban. Fuskanta da qafafuwanta su kumburu, duk shape dinta sun bace bayan ta haihu, tafara shayar da yaronka nono, tumbinta ya yankwane, nononta su kwanta tazama kamar wata yar shekaru 50 zuwa 60….

Yanzu maimakon ka tallafa mata wajen dawo mata kyawunta da (shape dinta) da nonon data shayar da danka suka kwanta, da tumbinta daya yankwane, sai kawai cikin sauki kayi watsi da ita….

Ka tsani kamanninta, wani lokacin kana basarwa idan ka ganta. A hankali har tsanarta da kakeyi ya fito fili kana cewa da ita: “Bana bukatar ganin ki”

Mr Man ka manta ne da yadda ka dakko ta gidan iyayenta?

Ka Manta da cewa kai ka yage mata tantanin budurci?

Ka manta da cewa Nonuwanta da suke bawa duk wani namiji Mai lpy sha’awa kai ka kwantar dasu?

Wai ka manta Alh wane da wane duk Sun fika kudi da abubuwan more rayuwa, amma ta zabe ka fiye dasu?

Ka manta ne, Usman Ahmad Haidar duk Sun fika kyawon halitta amma ta zabe ka sama dasu?

To ka sani Allah dai shine lauyan da zai Tsayawa mata a Ranar lahira.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!