Cikakken bayani game da Google ADSENSE
Assalamu Alaikum yan uwa barkan mu da sake saduwa daku a cikin sabon shirin namu wanda yake zuwa kai tsaye daga howgist.com in shaa Allahu yau zamu tattauna ne game da abinda ake kira Google AdSense, yanda ake aiki dashi da kuma yanda ake samun kudi dashi a shafukan yanar gizo.
Google Adsense wani shirine da babba kuma sanannen kamfanin nan na fasaha wato Google ta kirkira kuma yake karkashin kulawarta, mutum zai iya shiga wannan shirin ta hanyar yin register a shafinsu wanda zamuyi bayani dalla dalla a mako mai zuwa yadda akeyi in mai dukka ya kaimu wanda yin hakan yakan bawa mutum damar saka talla a shafinsa na yanar gizo kama daga hoto, sauti ko kuma hoto masu motsi wanda aka fi sani da video a turance. Mutum zai sami kudi a duk lokacin da wani ya danna wannan tallar ko kuma ya sami mutane da dama suka ziyarci shafinsa na yanar gizo.
Wannan shirin yana daya daga cikin manyan shafuka dake bawa mutum damar samun kudi a shafinsu na rubutun ra’ayin kai a yanar gizo a kowace kasa a fadin duniyar nan. Abun mamaki dake tattare da wannan shirin anan itace yana daga cikin hanyoyi masu sauki da mutum zai bi wajen samun makudan kudi a yanar gizo ta hanayar amfani da shafinsa. Shi wannan tallar yana zuwa ne a girma daban daban da kuma sura daban daban abinda kake bukata kawai shine zabar iya san ranka sannan sai ka cope wani dan code wanda zaka saka a shafinka dan watsa tallace tallace su cikin lumana.
Shi dai wanna shirin an yisa ne kawai wa masu rubutun ra’ayin kai a yanar gizo sannan duk wata tallace tallace tana zuwa ne daga wata shiri wanda ake masa lak’ani da Google AdWords wanda itama wata shirine da mutum zai biya kudi sannan ya saka hajarsa dan tallatawa.
Shin Yaushe kuma ya ya za’a biyani?
Indai wannan ne tambayar dake cikin ranka na tanadar maka da cikakkiyar amsa. Dan nasan ka da bala’in son kudi afuwan ba kai kadai ba kowa ma hake yake a jininsa. Google AdSense dai yana aiki ne da dalar amurka, sabida tushensu a can kasar amurka yake sannan duk lokacin da adadin kudin da ka samu ya kai koya zarce dala dari wato $100 kamfanin google zata tura maka kudin a sabon wata mai makawa misali a dadin kudina ya cika dala dari da ashirin da biyar $125 a kwanan wata shabiyar a watan satomba to bazan sami kudina ba a wannan watar sai wata mai kamawa wato daya ga watan October zasu tura min kudina zuwa cikin banki na basai lallai nan gida Nigeria ba kowace kasa kake in dai a duniyar nan take zasu turawa maka a barka; amma wasu bankuna zasu juya maka ita zuwa kudin kasar ka kamar anan Nigeria in an tura maka kudin zuwa banki ita bankin da kanta zata canza zuwa kudin kasar mu wato naira amma wannan bai zama wajibunba ya dai dan ganane da yanda ka bude account din in dai wa kasa Nigeria kawai ne to sai kudin kasar kawai zai shiga amma kuma in na duniya gaba daya yadda wasu masu kudir suke ka bude to akwai yakinin cewa kudin zata zauna a matsayinta na dala zaka kuma iya zara kowace lokaci a kuma ko ina.
Ingantattun hanyoyi da Google AdSense ke tura kudi
- Cheque: kamfanin google zasu juya kudin ka daga dallar amurka zuwa kudin kasar ka wanda zasu turo maka da cheque har cikin gida koda kuma a kauye kake sai de wannan hayar tana amfanine a kasashe arba’in 40 kawai a fadin duniyar gaba daya.
Amma kuma wannan hanyar tana da yan wasu matsaloli a tattare da ita wasu daga cikinsu sun kunshi za’a iya tura maka cheque kafin bankin ka su samar maka da kudinka zai dauki lokaci mai tsawo kuma maganar gaskiya zaka ji da jiki dan kullum ka ringa zirga zirga kenan kaine daga nan zuwa can daga sama zuwa kasa ba wai fa can samar iska nake nufi ba dan t’sanin ta karye jiya yan sama sama dai nake nufi.
Amma kuma in ka kasance dan mai son a sani ne irin abokina (wai so shi yake duk yan unguwarsu su san cewar shi fa ba karamin mutum bane dan har yan kasar waje har ita ma kamfanin google ta san da zamar shi) to wannan hanyar ita ta dace da kai amma bari na gaya muku wani abu Allah yasa kar yajini wannan abokin nawan ya ta yawo a banki dan ayi masa aikin kudin amma ina ya gaza karshe ya gaji ya bari, amma dai yata cewa mutane yayi nasarar samu bayan yace na rufa masa asiri.
- Electronic Transfer: wannan dayar hanyar ce kuma ingattaciya wanda su kamfanin google zasu turo maka da kudinka ta hanyar transfer zuwa cikin bankinka ba tare da ka sha wata wahala tsiya ba ko kuma ka takura kanka kuma a ko ina a cikin fadin duniyar nan.
A wasu makonni masu zuwa insha Allahu zanyi cikkakiyar jawabin yadda ake register da yadda ake sa shi code din a shafi na blogger ko wordpress. Kada ku mata kuyi sharing na wannan post din zuwa ga yan uwanku dan su amfana.