Dama Ta Samu: Gwamnatin Tarayya Zata Horor Da Matasa Miliyan 3 A Harkokin Fasaha Tare Da Basu Tallafi

Assalamu alaikum warahamatullah barkanmu da wannan lokaci da fatan kowa yana cikin koshin lafiya.

Gwamnatin Tarayya ta Kudiri aniyar Horar da Matasa Miliyan 3 akan harkokin Fasahar Zamani karkashin Hukumar NITDA amma har yanzu matasan Arewa basu cike ba

Kamar yadda aka saba mu matasan Arewa duk sanda aka bijiro da wani sabon al’amari na cigaban ƙasa mu ake bari a baya, sai bayan angama cin morariyar abin sai mu dawo muna cewa an cuce mu, lokaci ya yi da zamu daina jifan juna da laifuka, mu miƙe tsaya ka’in da na’in don a dama damu.

Hukumar NITDA wadda ke da alhaki wajen kula da abinda ya shafi ‘information Technology’ ta ƙudiri horarsa da Matasa Miliyan 3 don kwarewa a fannonin Ilimin Na’ura mai Kwakwalwa ‘Computer’. Za’a fara da kaso na farko wanda shine mutum 30,000, kuma za’a fara da wadannan fannuka kamar haka:-

1. Software Development
2. UI/UX Design
3. Data analysis and Visualization
4. Quality Assurance
5. Project Management
6.Data Science
7. Animation
8. AI/Machine Learning
9. Cyber Security
10. Game Development
11.  Cloud Computing
12. Dev Ops

Wanda yake son ya koya ko kuma yana da kwarewa akan daya ko wasu daga cikin wannan fanni zai iya cikewa ya nemi ya koya ko kuma ya nemi ya zama mai koyarwa don gwamati ta biya shi kuɗi.

Ga mai koya, wannan dama ce da zai samu damar karbar shaidar horaswa daga NiTDA (Certificate) kuma ya samu ilimin da zai iya Dogara da kansa, dama kuma harkar IT tana bukatar samun ‘Certificate’ daga wani waje wanda aka yarda dashi.

Duniya tayi nisa akan wannan fanni, a kasashen turai miliyayoyin kudi ake biyan wanda yake da ilimi akan wannan fannuka.

Ga wanda yake so ya koyar da wannan fanni ance gwamnatin tarayya takan biya maƙudan kudi muddin kana da waje (office ko Centre) da kuma shaidar da tabbacin kana da wannan ilimi (certificate), zaka iya samun yakai miliyan guda (ko sama da haka ko ƙasa da haka) ga duk bangaren da ka koyar guda 1, kaga kuwa akwao harka.

Domin cikewa ga wanda zai koyar (Trainer) da daya daga cikin ilimin nan ka ziyarci
👇

https://provider.3mtt.training/

Ga wanda kuma suke son su koya (Fellow) zasu iya danna wannan dake kasa
👇

https://fellow.3mtt.training/

Ga Kungiya ko Kamfani wanda suke so ku tallafa (Partner) wajen shiga wannan aiki ko a tallata musu hajarsu zasu iya danna kasa
👇

https://partner.3mtt.training/

Mun samu tabbaci daga wasu daga cikin masu kula da wannan aiki, sun tabbatar da cewa a cikin wadanda suka yi rejista ko kaso 20 (20%) cikin dari babu na asalin yan Arewa, don haka muke kira ga kowa da kowa da mu yaɗa wannan sako don matasanmu su mora, ko da kai baka bukata, ta yiwu wani wanda ka turawa zai bukata. Arewa an barmu a baya, mufarka.

Allah ya bamu nasara ya taimake mu.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!