Ga Wata Sabuwar Sanarwa Daga Hukumar Kidaya Census Adhoc
Ina taya murna ga applicants da hukumar kidaya ta kasa #NPCCENSUS ta amince dasu domin basu aikin wacin gadi bangaran enumerators da supervisor ranar 29 ga watan ukun da muke ciki zaa fara gudanarwa da kidayar jama’a sai dai kafin nan dole applicant ya samu training .
Ranar 13 ga watan uku hukumar kidaya zata fara horar da ma’aikatan wucin gadi bangaran enumerators da supervisor karbar horo dole ne ga duk mai son cin gajiyar shirin nan don haka yana da kyau mutukar anyi maka approval kake shiga Email address din ka da kayi rijista akai akai ta nan ne zaa gayyace duk wanda ya samu Approval.
Abu mafi mahimmanci game da duk wanda ya samu Approval ya samu aikin nan mutukar Enumerators ka cike ko Supervisor.ku sane aikin kidayar nan ba kamar aikin zabe bane mutanan da sukayi online daban mutane da sukayi training daban sannan mutanan da aka diba Suka gudanar da aikin suma daban saboda an saka son zuciya .
Babu wani wanda ya isa ya cire sunan ku mutukar kun samu Approval kuma kun shigar da bayanin bankin ku ,abu na biyu daya kamata ace kun kara sane shine duk wanda ya nemi aikin kidayar nan akwai NPC-CE-ID da hukumar take baiwa duk wanda ya nema bayan ya samu zai shigar da bayanin asusun ajiyar sa ta bankin .babu wani da zai amfani da NPC-CE-ID din wani .
Idan kun halatarci karbar horo wato training tabbatar ka rubuta NPC-CE-ID da NIN NUMBER dinka itace shaidar da zata nuna cewa ka halatarci training da zarar hukumar ta soma biyan kudin allowance zaka samu naka in Sha Allahu.
©️Ahmed El-rufai Idris
Kaduna State Coordinator Zumunta Youth Awarenesses Forum