GYARAN JIKI DOMIN AMARE CIKIN SAUKI
- Ga kuma wani hadin duk na gyaran fatar jiki shi ma wannan hadi ne na musamman
- wanda ya ke sa fatar mace ta zamo tana tare da shauki da laushi kai har ma zaki ji
- jikin ki yana wani damshi damshi wannan hadi ne da yawanci amare ka wai ake yi
- wa shi. Za ku tanadi ababen kamar haka
- Ayaba
- Lemon tsami
- Tataciyar madara
- Kwai daya
Za ku sami ayaba mai kyau ku bare k matse da hannuku, ko ku markada a
blenda ya yi laushi, sai ku zuba tataciyar madara ku fasa kwai kamar guda daya
amma farin zaku zuba sai ku matse lemoun tsami ku gauraye shi ku shafa a
jikin ku ya samu kamar tsayin awa daya, sai uk yi wanka da ruwan zafi, idan har
kuka lazinci yin haka kamar kwana uku za ku sha mamaki.