hanyar da hackas sukebi wajan hacking na WhatsApp din mutane ya kamata ku sansu kuma ku kiyaye

Asalamualaikum barkanmu da sake saduwa A Wannan lokaci zakaji ana yawan yiwa mutane hacking na whatsapp, hanyoyi biyu masu hacking din whatsapp suke bi wajen yiwa mutane hacking na whatsapp dinsu gasu kamar haka

Hanya ta farko idan wani yana so yayi hacking din whatsapp dinka zai kiraka ne a waya yace maka daka kamfanin whatsapp ne suna yima gyara a whatsapp dinka dan haka zasu turoma Comparmation Code yanzu zasu ce maka ka fada musu wannan Comparmation Code din da suka turamaka kana fada musu shikenan sunyi hacking din whatsapp dinka whatsapp din dake wayarka zai dena budewa gabaki daya zai koma bude a wayar su zasu dinga ganin dukkan nin chat din da kake da mutane sannan zasu dinga yin chat dasu a matsayin kaine, wannan matsalar idan ta faru koda kayiwa kamfani whatsapp report zai iya daukar 2weeks ma’ana sati biyu kafin whatsapp dinka ya dawo.

Hanya ta biyu suna yin amfani da wani Application mai suna Whatsweb mai hacking din zai bude shi a wayar sa zai danna inda akasa Whatsweb idan danna wa zai kawo masa Code wanda ake scanning dinsa mai hacking din zai iya kasancewa abokin kane ko kuma ya sanka zai karbi wayarka ne idan ya karba zai shiga cikin whatsapp dinka yana shiga zai danna wannan digo digon guda uku na fuskar whatsapp dinka yana danna wa zai kawo masa rubutu da yawa zai shiga inda akasa (Linked Devices) yana shiga kawo Camerar da ake Scanning Code da ita  idan baku manta a baya ya bude Application mai suna Whatsweb wannan App din ya bayyana masan Code wanda ake yin scanning din sa to kaga kenan zai dauki wayar wayarka yayi scanning din wannan code din dake wayarsa yana yin haka shikenan yayi hacking din whatsapp dinka baka sani ba kaga kenan yayi hacking din whatsap dinka ta cikin wayarsa, amma zaka dinga yin chat da whatsapp dinka saidai kuma wanda yayin hacking din whatsapp dinka yana ganin dukkan nin chat din da kukeyi da mutane ta cikin wannan App din dake wayarsa, wannan ba kamar hanya ta farko bace da zai kwace ma whatsapp din gabaki daya ba.

Dan haka yan uwa sai a kiyaye wadan nan hanyoyi karka yarda wani ya kira ka a waya yace ka turama Compermation Code na whatsapp dinka ka turama sa sannan kada ka yarda wani ya ari wayarka ya shigamar whatsapp.

KU cigaba da kasancewa damu a koda yaushe domin samun abubuwa kimiyya da fasaha

2mungode

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!