Yadda Zaku Samu Kudi Ta Hanyar Kiran Waya Da Kukeyi Da Layin MTN

Duk wayar da kakeyi idan har Layin MTN kake using kuma kana tsarin MTN Pulse to kuɗi kake samu kaima

Eh, ƙwarai ina magana ne akan “Pulse Point” idan har kana tsarin MTN mai suna “MTN Pulse Tariff Plan” to nasan zaka fahimci me nake nufi da “Pulse Point”.

Shi “MTN Pulse Points” ƙyauta ce daga kamfanin MTN da suke bayar da ita ga duk mai amfani da layin MTN kuma yana cikin tsarin “MTN Pulse” ana samun wannan ƙyautar ne a duk sanda kayi waya koda kuwa ta minti ɗaya ce, kana gamawa zasu turo maka da “Points” ɗin da kasamu a wannan mintin da kayi kana waya, ana amfani da wannan Points da suke bayarwa wurin siyen “Data Plans”, “Night Plans”, “IG & Tiktok Plans”, da wannan Point duk zaka iya siyen data ta sati-sati, ko wata-wata, data har ta 500 ko 1000 zaka iya siye da wannan ƙyautar Points ɗin da sukeyi maka.

Tabbas idan kana MTN Pulse nasan kana samun waɗannan Points ɗin ƙila ma ba tareda kasani ba, mai yiwuwa ma ƙila kanada sama da 500 points amma ka rasa amfaninta, to lallai yau zakasan amfaninta kuma zaka siya data da abunka.

Farko idan kanason kasan adadin Points ɗin da gareka domin kasan adadin data ɗin da kakeda ikon siye, zaka danna *406# idan ya baka Options sai ka zaɓi Lamba “7” zai sake baka zaɓi sai ka zaɓi Lamba “1” daganan shikenan zai nuna maka yawan adadin Points ɗin da gareka.
Wannan Point ɗin daidai yake da Naira, Ma’ana Point guda ɗaya (1) daidai yake da Naira ɗaya (N1) kaga kenan Point guda 100 daidai yake da Naira 100 har zuwa sama.

Hakan yana nuna maka cewa idan kanada Point guda 100 zaka iya siyen data na naira 100, haka zalika idan Point ɗinka yakai 500 zaka iya siyen data ta 500 da sauransu.

Idan ka duba kaga kanada Points koda guda 50 ne tunda akwai data ta Naira 50 zaka iya siyen ta ya danganta dai da Points ɗin da kagani, ga hanyar da ake siyen Data ɗin da Points kamar haka: zaka danna *406# yana buɗewa zai baka Options guda “8” sai ka zaɓi wurin da aka rubuta “Pulse Points” kana dannawa shima zai baka Options guda “5” sai ka zaɓi na farko wato “Redeem Data Bundles” daganan zai baka zaɓin wace irin data kakeso, “Daily” “Weekly” “Monthly”. Sai ka zaɓa, bayan ka zaɓa zasu sake baka Option ɗin cewa ta nawa kakeso kasiya da Point ɗin naka sai ka zaɓa, bayan ka zaɓa zasu baka wani Option guda biyu (Auto Renew or One-Off) sai ka zaɓi na 2 wato “One-Off” shikenan zasu ƙara baka Options guda biyu na farko zasu ce maka shin da Point ɗinka kakeson siyen data ɗin, kokuwa da katin wayarka tareda points ɗin? Kawai sai ka zaɓi na farkon da yace da point ɗinka kawai kakeson siye. (With Point Only)

Kana dannawa shikenan zakaga sun turo maka Message na data ɗin da kasiya da Point naka.

Allah Yataimaka..

©Salisu Abdurrazak Saheel

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!