Hukumar NiTDA Ta Sake Bude Shafinta Domin Horar Da Matasa A Harkar AI Developers Group Training Cohort 12
Assalamu alaikum warahamatullah barkanmu da sake kasancewa daku a wannan shafin namu mai albarka da fatan kowa yana cikin koshin lafiya.
Hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa wato NiTDA ta sake bude shafin ta domin bawa matasa horo a bangaren AI Developers Group Training Cohort 12
Wadanda Zasu Iya shiga sune matasa mata da maza masu shekaru daga 15 zuwa sama Sannan kuma membobin NYSC Corps, Dalibai, Digiri, da Masu sha’awar Fasaha. Duk zasu iya shiga
Shi de wannan shirin mazauna garin Abuja da kuma kewayenta zasu nema da kuma dukkan wanda yake da sha’awar shiga zai iya shiga
Tsarin shiga aikin tsaruka biyu ne, akwai na yan koyo akwai kuma na wadanda suka kware
Sabo da haka saika shiga ka cika
Matakin farko: bit.ly/3PvvsoE
Matakin tsakiya: bit.ly/3EVf3Fc
Za’a rufe ranar: 6 ga Oktoba, 2023.
Kada ku rasa wannan damar don haɓaka ƙwarewar AI!