Jamb Ta Soke Jarabawar Dalibai 817 Na 2023

Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire ta Najeriya, JAMB, ta ce ta soke rijistar dalibai sama da 817 da za su rubuta jarrabawar ta 2023, saboda saba wasu ka’idoji.

Hukumar ta ce ta yi hakan ne saboda wasu abubuwa da ta gano da suka saba doka, kamar amfani da bayanan mai rijistar da suka bambanta da hoton zanen yatsu na wani daban da mai rijistar.

Shugaban hukumar jarrabawar Farfesa Ishaq Oloyede, wanda jaridar Punch ta ruwaito cewa ya bayyana haka a wata sanarwa a yau Laraba, ta ce, wasu jami’ai a wasu cibiyoyin rijistar 178 sun rika sanya hoton zanen yatsunsu wajen yi wa dalibai rijistar.

Sai dai ya ce korafin da wasu daga cikin daliban ke yi shi ne na’ura ta ki daukan hoton nasu yatsun saboda ya yi zafi ko wani abu saboda haka sai jami’an su sanya nasu domin kammala musu rijistar.

A dangane da haka, tsohon shugaban Jami’ar Ilorin din ya ce, ba za su iya tantance wadanda suka yi hakan da kyakkyawar niyya ba da kuma masu niyyar magudi ta yadda wasu za su yi musu jarrabawar, saboda haka suka soke gaba dayan wadanda aka samu ire-iren wadannan saba ka’ida.

Sai dai tsohon malamin ya ce, hukumar ta JAMB ta bayar da dama ga daliban da abin ya shafa da su sake yin rijistar amma cibiyar da suka yi rijistar ce za ta dauki nauyin biyan kudin.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!