Karatu Zuwa Kasashen Waje Kyauta Daga Gwamnatin Tarayyar Nigeria /2023
Scholarship ta gwamnatin tarayyar Nigeria
Assalamu Alaikum Warahmatullah
En uwa barkanmu da wannan lokaci, barkanmu da sake kasancewa daku a wani sabon shirin.
Shirin bayar da scholarship ta gwamnatin tarayyar Nigeria karkashin jagorancin ministan ilimi Mallam Adamu Adamu, yana gayyatar daukacin daliban Nigeria masu sha’awar shiga shirin bayar da scholarship ta gwamnatin tarayya 2023/2024.
Karatun Undergraduate (UG) za’a tura su zuwa kasar Russia, Morocco, Hungary, Egypt da Venezuela;
• Karatun Postgraduate (PG) za’a kaisu zuwa kasar Russia (ga wadanda sukayi karatun digirinsu na farko a kasar ta Russia), China, Hungary, Serbia da kuma Romania.
A takaice
Fagagen Karatun da Ake Bukata:
Matakin Undergraduate — Geology, Agriculture, Engineering, Sciences, Mathematics, Environmental Sciences, Sports, Law, Social Sciences, Biotechnology, Architecture, Medicine, Pilot Engineering da Neurologist.
Matakin Postgraduate (wato masters da PhD) a kowane mataki ko fagen karatu.
Requirements
A. Scholarship ta Undergraduate: Dukkan applicant na undergraduate degree dole su mallaki mafi karacin maki 7 na distinction (kamar A da B) a makin karatun secondry, WASSCE/WAEC (May/June) kawai a subjects din da suke da alaqa da fannin karatunka daya hada da English da Mathematics. Kada certificate din ya haura shekaru 2 (2021 & 2022).
• Scholarship ta Postgraduate: Dukkan applicants masu karatun masters ko PhD dole su mallaki kwalin digiri tare da 1st class ko a kalla 2nd class upper.
Dukkan applicants dole ne su kammala N.Y.S.C sannan kada applicants ya haura shekaru 35 na masters, sai shekaru 40 na masu karatun PhD.
- Certificate na N.Y.S.C kadai ake karba; da kuma
- Takardar released ga ma’aikaci.
Takardun Da Ake Bukata
Duk wani candidate da akayi nominating dinsa za’a bukaci daya mika wadannan takardun zuwa Federal Scholarship Board:
• Asalin kwafin takardun karatu.
• Shafin bayani na passport din kasar waje na yanzu;
• Report na tabbacin lafiya daga asibitin gwamnati.
• Certificate na haihuwa & indigene letter
• Certificate na clearance daga ofishin ‘yan sanda idan ya samu.
Yadda za’a Nema
• Ku ziyarci shafin yanar gizo na http://www.education.gov.ng/ sannan ku danna kan Federal Scholarship Board akan shafin:
• Ku karanta dukkan bayanan sannan ku cike form din application online ? http://fsbn.com.ng/applicants/auth/register/45480
• Sai kuyi printing na application form din
Lokacin Rufewa
January 6, 2023
Wannan shine link din?
Allah yabada sa’a