Android Tricks: Yadda Zaka Kulle Wayar Abokinka Ta Wayar Ka Koda Wayar Ka Keypad Ce.

A kwanakin baya nai muku Alkawarin zanyi Muku posting da cikakken bayani akan Yadda zaka saka Security Codes a wata wayar Ta cikin wayar ka,

Idan abokaina basu manta ba, a shekarun baya nasha kawo muku abubuwan Kimiyya da fasaha ire iren wadannam abubuwan, domin kuwa idan zamu i’ya tunawa har shi wannam dim da zanyi Posting Yanzu na taba rubutu akansa a Shekarar 2017.

Banyi wannan posting din domin wasu suyi amfani da hakan wajen Cutar da wasu, ko kuma zalunci ba. Hasali ma an kirkiri wannan Manhajar ce, domin dalilai kamar haka 👇

1:- Dalili na farko: da akwai wasu lokuta da Mutane ke manta wayar su, a Gida ko wani Wajen wanda basaso a dauki wayar tasu a dinga musu bincike.

2:- Dalili na Biyu: Haka kuma da akwai Lokacin da wani Abokin ka sai Ya dauki wayar taka kai kuma ba kaso ko da Yasan Security Codes dinka zaka iya amfani da wannan ka Kulle wayar ka, ta cikin wata Wayar.

3:- Ko ka manta da wayar a wani waje amma baka Kashe Data/Wifi ka ba

4:= Ko yayin da wayar bata kusa da kai bakaso idan an kira Wayar tai kara

Wadannan sune kadan daga cikin Amfanin Wannan manhaja, amma mafi abunda akafi Yi dashi shine Kulle wayar ta cikin wata Wayar.

Kafin kayi wannan aiki dole akwai wasu matakai da zakabi

Da farko ka dauko wannan Application din 👇

http://www.mediafire.com/file/in1tpb4z5f36u88/Remote+Phone+Access.apk/file

Bayan ka dauko shi saika tura shi a wayar da kakeso ka dinga #Control dimta bayan Ya bude zaka ga wajen da akace

ENTER PASSCODES: anam zaka saia Numbobi guda4 kowane iri

Bayan ka gama zai bude saika shiga

General Setting
Primary Email: kasa Phone Number ka

Trusted Mobile Number: Kasa number da kakeso kayi amfani dashi wajen Sarrafa wayar misali: Phone number layin da kakeso ka dinga kulle wayar dashi koda layin Yana waya Keypad ce…. Daga nan ka tava (Enable Remote Access)
sai kayi kasa ka tava

Activate this device administrator

Daga nan saika fito ka gama 👌

Idan kanaso ka gwada aikin ga Command din da zakai amfani da su

👇

Idan kanaso ka Kulle wayar ne saika, shiga wajen tura Text Message din wancen wayar da ka saka Phone Number nan a wajen Trusted Phone Number: ka rubuta wadannan words din ka tura 👇

EnableAccess Passcode dinka: saika tura

Misali

EnableAccess 4347

Kana tura wannan Command din koda wayar tasa Ya saita wani Security Codes din daban, anan take wayar zata rufe zata nuna masa Yasa codes kuma koda Yasa bazata bude ba dole sai dai wannan Passcode din naka daka Tura ta Message ta wayar ka, kuma. Koda Wayar taka Keypad ce indai ka tura Aradu saita kulle… Shin idan wancen wayar ta fada Security wasu numbobi ne zasu iya bude ta?

Nasan zakumin wannan Tambayar numbobin nan daka saita wato Passcode guda4 da nace sune kadai zasu bude ta.

Bawai iya Security ne kadai zaka iya jefa wayar wani ba harda, zaka iya sa wayar ta dinga Rink haka kawai… Idan kanaso kasa wayar tasa ta dinga Ring saika je wajen tura Message a wayar ka ka Tura

👇
Ring Passcode dinka

Anan take zata dinga Kara

Da akwai sauran abubuwa da zaka sa Wayar wani ta dinga Yi ta hanyar tura Command ta Wayar ka.

Duk Wanda Yayi Amfani da Wannan Hanyar Ya cutar Da Wani Allah Ya Isa, na baku ne kawai Domin kusan Anayi, lolz… Da kuma masu cika abaki.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!