MTN USER’S GA TSARIN YIN KIRA MAI SAUKI DA ₦100 KACAL ZAKAI TSAWON MINTI 20 KUNA SHEKE WAYA

Yadda za kai kira har na tsawon mintuna ashirin(20) akan layin ka na mtn, bayan antoshe hanyar Rccg wato Cug na layin Airtel.

Ku biyomu a sannu a sannu ku karanta rubutun nan tun daga farko har karshe zaku fahimce mu da yadda akeyi cikin sauki.

Assalamu Alaikum ‘yan uwa masoyan shafin mu mai albarka, yau munzo muku da wata hanya da zata matukar birgeku sosai da sosai, kuma ita wannan hanyar mun samota ne daga layin Mtn dan a namu tunanin mutane sun fi amfani da Mtn fiye da Airtel yanzu, sabanin da mutane suna amfani da Airtel ne sosai saboda tsarin kiran garabasa da suke samu da Airtel akan kira har na tsawon mintuna 40 zuwa 50 ga duk wanda yake kan tsarin su na Rccg wato Cug.

To kamar yadda kuka sani cewa yanzu Airtel sun rufe hanyar yin kira da akeyi na Rccg wato Cug na tsawon mintuna 40 ko 50 akan ₦100 kacal.

To tabbas mutane da dama sunji rashin dadin rufe wannan hanya da’akai, mussamman ma ga masoya da wadanda ke kiran mutanen dake kasashen ketare.

To hakan tasa wasu suka rage yawan yin Kiraye kiraye da wayoyin su, mussamman masoya.

Bayan dogon zurfafa bincike da mukai akan hakan Allah yataimake mu yakuma bamu sa’ah wajen samowa wata hanya mai dan saukin kira duk da batakai wancan ta Airtel sauki ba amman dai munsan cewa insha Allah za’a rage da’ita Kuma hanyar zata taimaka sosai, wajen sanya mutane sudawo suci gaba da kiraye-kirayen da suka saba sunayi abaya da layin Airtel Rccg wato Cug.

Wani abin birgewar ma da hanyar da muka samo din shine sai muka samo hanyar a layin Mtn Wanda mutane sukafi aiki dashi.

HANYAR KUWA ITACE”

YADDA ZAKAI KIRA DA LAYIN MTN HAR TSAWON MINTUNA ASHIRIN (20) DA NAIRA DARIN KA KACAL ₦100.”

Dan haka Maison ganin yadda akeyi ga bayanan Kamar haka:

Abubuwan da ake buƙata-

? Layin MTN (Mtn sim card)

? Kasancewa a tsarin Beta Talk (beta-talk plan)

? Sai Kuma katin waya na naira dari ₦100 kacal wato(Recharge card)

Idan baka cikin tsarin Beta talk ga yadda zakai kashiga

Zaka danna *123*2*1*1#.

Tsarin Beta Talk suna ba da bonus ₦300 akan duk kati na naira dari ₦100 da ka saka, kaga riba biyu kenan ga tsarin da zamu koyama ga Kuma bonus din dari uku akan duk naira dari daka saka

Bayan ka shiga tsarin Beta-Talk din sai ka saka katin waya na naira dari ₦100, inkuma kana dashi a wayar kama shikenan.

SAI KUMA YADDA ZAKA JUYA NAIRA DARIN KA ₦100 TA KOMA MINTUNA 20 DIN KO KUMA NACE MINTUNA GOMA SHABIYU 12 DAN WANI LAYIN BASA BAYARWA YAKAI MINTUNA 20 WANI SUNA BASHI MINTUNA GOMA 12 NE.

Za kazo zaka danna *567*119*1*1#

sai ka danna alamar calling .

Idan Kuma kayi haka bai yi ba, sai ka je wajen message ka rubuta 100 sai ka tura zuwa 567, shikenan insha Alllah zaiyi.

Za su ba ka Zaɓi (option),

sai ka Zaɓi 1 ko 2.

Za su ba ka ₦120 da kuma 100Mb shikenan saika futo ka fara more kiran ka.

Amma kasani dan’uwa duk sanda ka saka kati sai kazo ka danna wadannan lambobin kamar yadda kayi na farko haka zakana yi.

Yanzu idan ka hada ka nada bonus na dari uki 300 yanzu kuma ka sami 120n, Insha Allah inka hada zasu kai mintuna 20 ko fiye da hakama.

Note: ka tabbatar da ƙaramar waya ka ke aiki da Layin, domin idan da babbar waya ka ke yi, da zarar datarka ta ƙare, bonus ɗinka na 300 za a fara ɗiba wajen yin browsen.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!