TSARABAR GIDAN MIJI
zan yi muku bayanin wadannan wurare tara don su kasance wani sirri a wurinku da za ku rika sarrafa mazajensu yayin jima’i cikin ruwan sanyi.
Wadannan wurare suna dauke da jijiyoyi wadanda kai tsaye suke aika sako zuwa kwakwalwa cikin kankanen lokaci. Wadannan wurare sun hada da:
- Cikin leben kasan baki
- Bakin namiji wuri ne da ke saurin aika sako zuwa kwakwalwa, kuma ga namiji yana saurin motsa masa sha’awa. Ba wai na sanar da ku wannan wurin sai kuma ku rika nacewa wajen tsotsar leben mijinku ba, hakan zai sanya ya ji kun gundure shi, lokaci zuwa lokaci za ku rika tsotsar wajen kasan lebe.
- A jikin lebe akwai wadansu kananan jijiyoyi wadanda suke motsa sha’awa cikin kankanen lokaci.
- Yadda za ku yi: A lokacin da kuke son motso da sha’awar mijinku, sai ku tura leben kasan bakin mijinku cikin bakinku, sannan ku rika amfani da tsinin harshenku kuna wasa da shi a kan fatar leben mai dauke da tarin kananan jijiyoyi masu isar da sako ga kwakwalwa. Za ku ci gaba da zuwa da dawowa da harshenku, inda hakan zai sanya mijinku ya tafi wata duniya cikin jin dadi. Zai rika jin kamar ana yi masa susa mai dadi a bakinsa ne.
- Wani abu da nake so in ja hankalinku shi ne, ku rika kula da bakinku, ma’ana ku tsaftace shi ta hanyar goge bakinku sau biyu ko uku a rana, ko kuma daf da lokacin da kuke so ku sumbaci mijinku don kada ya rika jin kyamarku, idan har kuna so tsotsar lebe ya kara armashi, to za ku iya sanya minti mai zaki a bakinku, walau lokacin da kuke tsotson ko kuma kafin, hakan zai sanya yawun bakinku ya kasance cikin zaki da kuma kamshin mintin.
- Gaban Wuya
- Yawancin mata ba su da masaniyar cewa wuya na motsa sha’awar namiji, wadanda suka sani kuma sun fi mayar da hankali wajen shafa gefen wuya ne, amma a zahirin gaskiya wurin da ya fi motsa wa namiji sha’awa a wuya shi ne gaban wayansa daidai saitin makogwaro, domin akwai kororon da ya wuce har zuwa cikin ciki, kuma wannan kororon yana dauke da jijiyoyin kanana da kai tsaye suke tura sako ga kwakwalwa,