wani sabon sirrin WhatsApp , WhatsApp tracker

Assalamu Alaikum barkanmu da sake saduwa daku a wanan lokacin cikin wannan sabon darasi a yau nazo muku da wani sabon Application wanda babu wani Application da zai temaka a whatsapp dinka sama dashi.
 

Sunan wannan sabon Application din What’s Tracker yana da matukar amfani zai temaka ma a whatsapp dinka sama da ko wanne irin Application, Application din yana da bangarori guda biyar gasu kamar haka

Searching profile 

Direct chat 

Profile visitor’s 

Restore deleted message

Statu

Searching profile bangare ne da zakai checking din number mutum ya gano ana whatsapp da ita ko ba’a whatsapp da ita.

Da farko zaka zabi County Code din lambar kasar da kakeso gane ana whatsapp da ita ko ba’a whatsapp da ita bayan ka zaba saika sa lambar wayar kasar bayan kasa lambar idan kana amfani da whatsapp biyu zasu kawoma su daka kasa saika zabi da wanne whatsapp zaka gano number daka sa ana whatsapp da ita ko ba’a whatsapp da ita bayan ka zaba daka gefe zakaga alamar Searching saika danna ta kana danna wa zasuyi Searching su gano ana whatsapp da ita ko ba’a whatsapp da ita idan ana whatsapp da ita zasu nuna ma idan ma ba’a whatsapp da idata zasu nuna ma.

Direct chat bangare ne da zaka turawa mutum message a whatsapp ba tare daka yi sevin din lambar saba.

Direct chat bangare ne da zai baka damar turawa dan uwanka message ma’ana sako a whatsapp ba tare da kayi serving din lambar sa a wayarka ba.

Akwai lokacin da wani dan uwanka zai iya baka lambar wani yace ka turama masa sako ta whatsapp dinka sakon hoto ne ko bidiyo kodai na wani message kai kuma baka san wannan mutumin ba idan kace sai kayi serving din lambar sa a wayarka zaka turamsa wannan sakon kana turamasa sakon shikenan lambar bata da amfani a wayarka tun bakasan wannan mutumin ba.

wannan bangare zai temaka ma wajan baka damar turawa mutum sako ta WhatsApp dinka ba tare dakayi serving lambar  sa ba. 

Da farko zaka zabi County Code din lambar kasar wanda kake son turawa sako a whatsapp ba tare dakayi serving din lambar wayarsa ba bayan ka zaba saika sa lambar wayar kasar bayan kasa lambar idan kana amfani da whatsapp biyu zasu kawoma su daka kasa saika zabi da wanne whatsapp kake son turamasa wannan sakon bayan ka zaba daka kasa zakaga inda akasa Enter Message a nan ne zaka rubuta sakon da kake son turamasa bayan ka gama rubuta sakon daka kasa zakaga alamar send saika danna ta kana dawa shikenan sakon zai tafi cikin sauki da kwanciyar hankali. 

Profile visitor’s bangare ne da zaka duba mutanen da suke kallon Profiles dinka na whatsapp kana shiga profile visitor’s zai kawoma bangarori guda uku Contact, Visited, Visitor’s.

Contact bangare ne da zai kawoma dukkanin lambobin mutanen ka wanda ake a whatsapp dasu.

Visitor’s bangare ne da zai kawoma adadin mutanen da suka zuciyarci profile dinka tare da sunan su da kuma hotunan su.

Restore deleted message bangare ne da zaka dawo da message din da aka turoma aka goge shi kafin ka gani a whatsapp.

Wannan bangare ne da zai tema kama wajan dawo da dukkanin messages din da aka turoma a WhatsApp wanda aka goge shi kafin ka gani irin wannan matsalar na faruwa zakaga kuna tsaka da chatting da mutum sai kaga ya turoma message kafin ka gani ya goge wannan message din idan har kana son ganin wannan message din daya turoma kuma ya goge shi kafin kagani zaka danna Restore deleted message kana danna wa zakaga inda akasa START RESTORING DELETED MESSAGES, Enables notifications access saika danna kana danna wa shikenan.

Yanzu duk wanda ya turoma message ya goge shi kafin kagani kana shigowa wannan bangaran zakaga wannan message din.

Status bangare ne da zakayi download din status din mutane na whatsapp.

Kamar yanda kuka sani dukk masu amfani da Normal whatsapp basa samun damar seving din status din mutane a kan wayoyin su saka makon kamfanin whatsapp basu tsara hakan ba akan Normal whatsapp saidai mutanen da suke amfani whatsapp wanda bana kamfanin whatsapp ba suna samun damar seving din status din mutane a kan wayoyin su kamar su GBWHATSAPP, OBWHATSAPP, FMWHATSAPP Da sauran su.

Kana shiga bangaran status zai kawoma status din mutane da kake chat dasu a whatsapp dinka sanan zasu baka dama ka kalli Status din kowa tare da baka damar yin download dinsa cikin sauki.

IDAN KANA SON DOWNLOAD DINSA 

Danna nan

Kai tsaye zaka danna gurin da nace ka danna ma’ana Danna nan kana dannawa zai kaika playstore to a nan ne zakayi download na Application din.

Yana gama download kai tsaye Application din zai fara install da kansa yana gama wa zai sauka akan wayarka shikenan saika fara amfani dashi. 

KU dai ku cigaba da kasancewa damu a koda yaushe domin samun abubuwa kimiyya da fasaha

mungode

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!